Matsalar Tsaro ta Kusa Zuwa Karshe a Kasar nan – Sifeto Janar na ‘Yan Sanda
Sabon sifeta janar na ‘yan sanda Najeriya ya jaddada cewa matsalar tsaro ta kusa zuwa karshe a kasar nan.
Ya sanar da hakan ne yayin bikin yaye wasu jami’an ‘yan sanda da suka samu horarwa a fanin shugabanci.
Ya ce hukumar ‘yan sandan Najeriya na aiki da sauran hukumomin tsaro wurin shawo kan matsalar.
Usman Baba, sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, ya ce jami’an tsaro na aiki tukuru wurin tabbatar da cewa sun shawo kan matsalar tsaron kasar nan, The Cable ta ruwaito.
Baba, wanda ya samu wakilcin DIG Danmallam Mohammed, ya sanar da hakan ne yayin da ake yayen ‘yan sandan da suka samu horo a bangaren shugabanci a kwalejin ‘yan sanda dake Jos.
Read Also:
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito, ya ce hukumar ‘yan sanda na aiki tukuru wurin dawo da zaman lafiya a dukkan sassan kasar nan kuma tana hada kai da sauran hukumomin tsaro.
Muna aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya tare da daidaituwa ta dawo dukkan sassan Najeriya,” yace.
“Tsaro al’amari ne ya da shafi kowa, ba zamu iya yin shi mu kadai ba. Muna yin iyakar kokarinmu tare da hada kai da sauran hukumomin tsaro wurin tabbatar da tsaro.
“Da izinin Ubangiji tare da taimakon ‘yan Najeriya, za mu shawo kan ta’addanci, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da dukkan wani nau’i na rashin tsaro a kasar nan.”
IGP ya sha alwashin horarwa za ta zama wani jigo na mulkinsa saboda hakan ne kawai zai tabbatar da ingancin tsaro a kasar nan.
A yayin nasiha ga wadanda suka samu horon, Baba ya kwatanta zanga-zangar EndSARS da abu mara dadi tare da kira ga jami’an da su sake duba hakkokin dan Adam yayin da zasu fara shugabanci.