NABTEB ta Saki Sakamakon Jarabawar Nuwamba/Disamba ta 2020

Sakamakon jarrabawar NABTEB na November/December ta 2020 ta fito.

Ifeoma Isiugo-Abanihe shugaban hukumar na kasa ne ta bada sanarwar.

Isiugo-Abanihe ta ce kashi 92.42% sun samu kredit biyar da fiye da haka.

Rajistara kuma shugaban hukumar shirya jarabawa na NABTEB, Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe ta sanar da cewa sakamakon jarrabawar da aka rubuta a watannin Nuwamba da Disamba na bara sun fito, rahiton The Nation.

Ta bayyana cewa kashi 75.72 cikin jimillar dalibai 21,175 da suka zana jarrabawar sun sama kredit biyar da abin da ya fi haka ciki har da darrusan Ingilishi da lissafi, yayin da kashi 92.42 cikin 100 wato dalibai 25,844 sun samu kredit biyar da lissafi da Ingilishi da wanda ba su da shi.

Isiugo-Abanihe ta bayyana hakan ne a jiya a hedkwatar hukumar na kasa da ke Benin a lokacin da ta ke sanar da sakamakon jarabawar tare da sauran manyan jami’an hukumar.

Ta yi kira a mayar da hankali kan ilimin fasaha da sana’i’i (TVET) a dukkan matakai a kasar tana mai cewa ilimin TVET din ne zai shirya matasa da manyan mutane a kasar su samu sana’o’in da za su iya dogara da kansu.

Isiugo-Abanihe ta ce duk da kallubalen annobar korona da ta janyo jinkiri wurin rubuta jarabawar May/June da November/December, NABTEB ta yi nasarar yin dukkan jarrabawan biyu daga baya. Ta ce hukumar za ta cigaba da gudanar da jarrabawa masu inganci a kowane shekara sannan za ta cigaba da inganta tsarin yin jarrabawar don magance magudi.

a ce, “A jarrabawar da ya fito, dalibai 250 wato kashi 0.77 cikin 100 ne aka samu da laifin magudin zabe. “Wannan cigaba ne idan aka kwatanta da dalibai 603 wato kashi 1.23 cikin 100 na daliban da suka rubuta jarabawar November/December 2019 da aka samu da laifin magudin jarrabawa.” Isiugo-Abanihe ta ce za a cigaba da yin rajistar jarrabawar NABTEB NBC/NTC har zuwa karshen watan Mayu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here