Covid-19: Gwamnatin Tarayya ta Sake Dawo da Dokar Takaita Fita

 

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta sake dawo da dokar takaita fita a dukkan kasar daga 12 na dare zuwa 4 na asuba domin dakile yaduwar annobar korona wato COVID-19, The Nation ta ruwaito.

Mukhtar Mohammed, manaja kula da yaduwar cuta na kasa ne ya sanar da hakan yayin jawabin da kwamitin shugaban kasa kan korona ta yi a Abuja.

Mohammed ya ce dokar takaita fitar za ta fara iki daga daren ranar Litinin.

Ya kuma ce daga ranar Talata za a rufe wuraren casu na dare, wuraren motsa jiki wato gym da sauran wuraren cinkoson mutane har zuwa wani lokaci nan gaba.

Ya ce an bada umurnin rage adadin mutanen da ke hallartar wuraren ibadah da kashi 50 cikin 100 yayin da za a cigaba da yin sauran taro da harkoki na gwamnati ta hanyar amfani da fasahar bidiyo na intanet.

Ya ce za a takaita duk wani taron mutane zuwa mutum 50 a kowane lokaci.

Ba za a bari mutane su shiga hukumomin gwamnati ba har sai suka saka takunkumin fuska.

Ya kara da cewa masu tafiya kasashen waje domin yin ayyuka masu muhimmanci suna iya yin hakan amma dole su bi dukkan dokokin dakile yaduwar cutar.

Kazalika, ya ce ba a takaita tafiye-tafiye a tsakanin jahohin Nigeria ba.

Ku saurari cikaken bayanin …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here