Matsayin Zanga- Zangar da Aka yi wa Buhari a Landan – Gwamna Matawalle
Gwamna Matawalle na jahar Zamfara ya kwatanta zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London a matsayin kaiwa arewa hari.
Tun watan Maris shugaba Buhari ya tafi London don a duba lafiyarsa kuma dama tunda ya dare kujerar shugaban kasa yake zuwa London akai-akai.
Wasu ‘yan Najeriya mazauna London sun yi zanga-zanga a can kuma sun yi hakan ne bisa yadda likitocin Najeriya suke yajin aiki gwamnati ta nuna musu halin ko-in-kula.
Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya kwatanta zanga-zangar da ‘yan Najeriya mazauna London suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin hari ne aka kaiwa arewa.
Tun a cikin watan Maris shugaban kasa ya bar Najeriya ya wuce London don a duba lafiyarsa.
Dama Buhari ya tsiri zuwa London tun da ya hau kujerar shugaban kasa a 2015, The Cable ta ruwaito.
Read Also:
Wasu ‘yan Najeriya mazauna London sun yi wa Buhari zanga-zanga bisa yajin aikin da likitocin Najeriya suke yi a Najeriya.
A wata takarda ta ranar Alhamis wacce Matawalle ya tura ya bayyana zanga-zangar a matsayin al’amari da wasu suka dauki nauyi, kuma wadanda suka shirya basu da wayewa.
Ya kuma ja kunne akan kaiwa ‘yan arewa hari da kuma sana’arsu a kudu.
“Na yi Allah wadai ta yadda kullum ake nuna tsana ga dan arewa kuma hakan ya zarce har suka kaiwa Buhari hari saboda masu zanga-zangar ba zasu iya boye tsana da hassadar da suke yi wa ‘yan arewa.
“Duk yadda suke fushi, abinda suka yi bai dace da dabi’a da wayewa da mutunci ba.
Yanzu haka tsanar shugaban kasa da arewa tana kara yawaita a garesu.
Gaskiya yin hakan bai dace ba ko kadan kuma daga masu zanga-zangar har masu daukar nauyinsu basu da wata daraja.
“Na tabbatar da shugaban kasa dan kudu ne ba zasu yi masa haka ba, kuma sun yi hakan ne musamman don su wulakanta shugaban kasa sakamakon ganin yawan ‘yan Najeriyan da suke zama a London.” Matawalle yace.