Shugaba Buhari na Goyan Bayan Mayar da Kujerar Shugabancin Kasar nan Kudu – Jigon APC
Wani jigon jam’iyyar APC ya bayyana cewa, Shugaba Buhari na goyon bayan mayar da kujerar shugabancin kasar nan kudu.
Ya bayyana haka ne yayin da yake bayyana kudurin yankin kudu maso gabas na samar da Shugaba daga kabilar Igbo.
A cewarsa, ya kamata a saki Nnamdi Kanu idan ana son yankin kudu ya zauna lafiya sannan a ba yankin shugabancin Najeriya a 2023.
Abuja – Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, wani jigo a jam’iyyar APC kuma Darakta Janar na Voice of Nigeria (VON), Mista Osita Okechukwu, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari a sirrance yana goyon bayan a samar da shugaban Najeriya daga yankin Igbo a zaben 2023.
Da yake magana da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, Okechukwu ya ce shugaba daga ‘yan kabilar Igbo ne zai kawo karshen tashe-tashen hankula da barazanar kungiyar IPOB a yankin Kudu maso Gabas.
A cewarsa:
Read Also:
“Shugaban kasa da sauran ’yan Najeriya sun yi shiru suna goyon bayan samar da shugaban Najeriya daga yankin Igbo a 2023, amma sun shuru kuma sun yi watsi da ra’ayin IPOB. Don haka, a karamar fahimta ta, tallafin da IPOB ke ba mu, zai kashe tsuntsaye biyu da dutse daya.”
Ya bayyana cewa wasu masu rike da madafun iko a siyasar Najeriya suna goyon bayan tsayar da shugaban kasa daga shiyyar Kudu Maso Gabas amma suna tsoron ayyukan kungiyar ta IPOB a shiyyar, don haka akwai bukatar kungiyar ta goyi bayan matsayar dattawa kan shugabancin Igbo.
Ya kara da cewa:
“Abinda na fahimta game da fafatukar IPOB shine kawo karshen wariyar da ake wa ‘yan kabilar Igbo.
Idan kuwa haka ne, shugaban mu na Najeriya na 2023 na daga yankin Ibo zai kawo karshen yakin basasan. ‘Yan Najeriya na jiran IPOB ta canza salo.”
“Ina kuma kira ga IPOB da ta tallafa wa Shugaban Najeriya na tsagin Igbo a 2023. Ina ganin goyon bayan IPOB zai kashe tsuntsaye biyu da dutse daya.
“Ina tare da Ohaneze Ndigbo, fitaccen Lauyan Tsarin Mulki kuma Shugaban Shugabannin Igbo, Farfesa Ben Nwabueze, da masu kishin kasa baki daya wajen yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da sakin jagoran IPOB da ke rike da shi.”
Ya kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba batun sakin shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Buhari ya shaidawa shugabannin Igbo da suka ziyarce shi a Aso Rock ranar Juma’a cewa zai duba bukatar a saki Kanu.