Yana da Kyau a Wasu Lokutan Maza su Riƙa bai wa Mata Jan Ragamar Siyasar ƙasar nan – Godswill Akpabio

 

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce akwai bukatar mata su rike madafun iko.

Ya ce ya kamata maza su riƙa komawa gefe domin bai wa mata damar ɗarewa kujerun siyasa.

Ya bayyana cewa adadin mata da ake da su a kujerun shugabanci ya yi kaɗan a halin da ake ciki.

FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce yana da kyau a wasu lokutan maza su riƙa bai wa mata jan ragamar siyasar ƙasar nan.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, a wajen wani taro na ƙasa da ƙasa kan rawar da mata ke takawa a shugabanci.

Cibiyar Nazarin Dokoki da Dimokuradiyya ta ƙasa (NILDS) ce ta shirya taron kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Akpabio ya ce akwai bukatar mata a siyasa

Akpabio ya bayyana cewa yana matuƙar sha’awar ganin mata riƙe da kujerun shugabanci na siyasa a Najeriya.

Sai dai yanayin siyasar da ake ciki a yanzu, ba su cika samun kujerun shugabancin ba sai dai a ba su muƙamai a gwamnati.

Shugaban ya ce adadin matan da yanzu haka ke a Majalisar Dattawan Najeriya sun yi kaɗan, inda yake ganin ya kyautu a ce sun wuce hakan.

Ya ƙara da cewa a bisa wannan dalilin ne yake ganin ya kamata maza su riƙa komawa gefe a wasu lokutan domin bai wa mata damar samun kujerun siyasa.

Akpabio ya nemi a yaƙi wariyar jinsi

Akpabio ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar a yaƙi wariyar jinsin da ake nunawa mata a cikin al’umma musamman yayin neman shugabanci.

Ya ce wannan wani abu ne da Cibiyar Nazarin Dokokin ya kamata ta yi da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin na kare haƙƙin mata kamar yadda The Punch ta wallafa.

Ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar a sauya yadda al’amura ke tafiya tun a baya da kuma yadda suke a yanzu, ta hanyar ƙarfafawa mata gwiwar su shiga siyasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com