Jahohin Najeriya da Maza Suka Fiya Auran Mata Fiye da ‘Daya

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka ba auren mata da yawa muhimmanci.

Da zaran dai mutum ya mallaki rufin asirin da zai iya duba mace fiye da daya toh baya shakkar kara aure musamman a yankin arewacin kasar.

Kebbi, Katsina da Kaduna ne kan gaba a jihohin da maza ke auren mata fiye da guda daya.

Auren mace fiye da guda daya abune da ya zama ruwan dare a Najeriya domin mutane da dama sun yarda cewa babu wani aibu dake tattare da tara mata idan har mutum na da halin daukar nauyin matan nasa na sunnah.

A kan haka, Legit.ng ta tattaro maku jihohin Najeriya inda maza daga shekaru 15 zuwa 49 suka mallaki akalla matan aure guda biyu.

1. Kebbi: 27.3% Jihar Kebbi ce ke da mafi yawan maza masu matan aure fiye da biyu. Alkaluman na a kan kaso 27.3 cikin 100.

2. Katsina: 26.3% Katsina ce ke bin sahun Kebbi kuma yawan mazan da ke da matan aure fiye da guda biyu a wannan jiha shine kaso 26.3 cikin 100.

3. Kaduna: 26.2% Kaduna ce ta uku a jerin jihohin da kaso 26.2 cikin 100.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here