MDD da Shugabannin ƙasashen Duniya Sun yi Allah Wadai da Hare-Haren Isra’ila a Gaza
Shugabannin ƙasashen duniya sun fara tofa albarkacin bakinsu kan hare-haren baya-bayan nan da Isra’ila ta kai a Gaza da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 400.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya ‘kaɗu’ da hare-haren, kuma ya yi kira da babbar murya da a mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar.
Read Also:
Firaminstan Australia Penny Wong ya ce ƙasarsa na buƙatar ɓangarorin biyu su mutunta tsagaita wutar, inda ya ce ”wajibi ne a kare dukkanin fararen hula”.
Shi kuwa mataimakin Firaministan Belgium, Maxime Prevot, ya yi alawadai ne da hare-haren, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin su tsaya kan yarjejeniyar, domin” kar a koma gidan jiya”.
Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov shi ma ya bayyana lamarin a matsayin abin damunwa.