Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-Wadai da Tarzomar da ta Barke a Chadi
Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarrayar Turai da kuma Amurka sun yi Allah-wadai da tarzomar da ta barke a Chadi lamarin da ya janyo rasuwar mutum 50 tare da jikkata wasu 300.
A wani mataki na ba zata, ofishin jakadancin Amurka a Chadi ba wai sanarwa kadai ta fitar ba na yin Allah-wadai da tashin hankalin na ranar Alhamis, amma kuma ya hada da wallafa hotuna a shafukan sada zumunta dauke da jakadan Amurka ya durkusa a kan titi kusa wadansu tsumokara duk jini.
Hakan na zuwa ne bayan da farar hula suka tarwatsa shingen bincike na jami’an tsaro sannan suka kashe mutum hudu a kusa da kofar shiga ofishin jakandancin.
Read Also:
Babu tabbas ko mutanen sun yi kokari kai hari ne a ofishin jakadancin na Amurka.
An saka dokar hana fita a N’djemena da wasu birane biyu a kasar.
‘Yan adawa sun ce za su ci gaba da zanga-zanga har sai an biya musu bukatunsu.
Suna son a gudanar da zabe ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban rikon kwarya, Mahamat Idriss Deby Itno ya dare mulkin kasar ne bayan an kashe mahaifinsa, Idriss Deby a watan Afrilun 2021.
Kuma ya yi alkawarin gudanar da zabe a cikin wattanni 18 amma a yanzu kuma ya kara lokacin zuwa shekara ta 2024.
A cikin sanarwar, ofishin jakadancin Amurka ta ce ta damu matuka kan yadda gwamnatin rikon kwarya ta soji ta yi burus da umurnin kungiyar tarrayar Afrika – AU na cewa mambobin gwamnatin rikon kwaryar kada su tsaya zabe a zabukan da ke tafe.