Me ya sa ake
ganin cancantar Atiku Abubakar fiye da Buhari a zaven 2019?

Fassarar
Rubutun
Fidelis Nwagwu

January 25, 2019

Cin hanci da rashawa a cikin kowace irin gwamnati ba
baqon abu ba ne, sai dai kowace irin gwamnati da ke mulki da ire-iren qalubalen
da take fuskanta game da cin hanci da rashawan. Sai dai ba inda aka fi ganin
munin haka kamar  inda a harkar gwamnati
ake xora mutane bisa muqamin da ba su cancanta ba ko kuma ware muhimman muqamai
domin ‘yan uwa da abokan arziki.

Ba wani abu ba ne sabo ga gwamnatocin Nijeriya su
dinga xauko waxanda ba su cancanta ba ko kuma ma ‘yan uwa da abokan arzikinsu
na kusa su xora kan wasu muqamai da ake ganin masu maiqo ne, amma a zamanin
gwamnatin shugaba Buhari, wannan yanayi na amfani da rashin cancanta ko ‘yan
uwantaka wajen gudanar da harkokin gwamnati, tuni ya wuce minsharrin ya kai
mahalaqa.Yanzu gwamnatin shugaba Buhari abin da ta sa gaba shi ne watsi da bin
dokoki da qa’idoji da cancanta da daidaito a wajen naxin muhimman muqamai,
wanda ke nuni da cewa mulki yana nema ya fi qarfinta. A halin da ake ciki yanzu
zarge-zarge sun yi yawa ko dai na cin hanci ko rashawa ko rashin amfani da
cancanta da shigo da ‘yan uwantaka saboda rashin tsari da kula da gwamnatin ba
ta da shi.

To sai dai wani abu da gwamnatin shugaba Buhari ba ta
sani ba ko kuma ta sani amma ta take sanin ba yadda za a yi a samu shugabanci
nagari ba tare da  an gina qasa bisa
tsarin tarbiyantar da al’umma da kawar da cin hanci da rashawa tare da haxin
gwiwar ‘yan kishin qasa bisa matakan da suka dace ba.

 A kodayaushe
‘yan kishin qasa a cikin al’umma suna yin da’awar tabbatar da ingantancen
tsarin mulki domin sauqaqa wa talakawa, ko ba komai ai gwamnati ko wace iri
tana gudana domin inganta rayuwar talakawa ne musamman ganin cewa talakkawan ne
ke zaven gwamnatin a bisa tsarin dimokuraxiya. Wannan ne ya sa cikin kowace
al’umma ake samun waxanda ba su ganin jariri a bayan mahaifiyarsa sai sun
tambayi wanene mahaifin nasa, duk gwamnatin da ta yi watsi da irin waxannan
mutane ko kuma ba ta xaukarsu da muhimmanci ko kuma bin shawarwarinsu tana iya
samun tarnaqi wajen gabatar da muhimman manufofinta.

Ganin cewa a gwamnatocin bayan na Nijeriya an sha fama
da matsalar gudanar da tsarin mulki na rashin ko ‘ yan uwanataka ba wanda ya yi
tsammanin hawan gwamnatin shugaba Buhari ta canji a 2015 wannan matsala za ta
sake kunno kai. Sai dai kusan shekara huxu bayan nan wace wainar aka toya
qarqashin jagorancin shugaba Buhari?

Da hawan gwamnatin shugaba Buhari kan mulki aka fara
zargin shugaban sojojin Najeriya a wancan lokaci Janar Azubuike Ehejirika kan
handama da babakere alhali shi kuma ya amshi ragama ne daga Janar Abdulrahaman
Dambazau, wanda ke nuni da cewa idan Janar Ehejirika yana da hannu cikin waccan
damalmala to haka ma Dambazau in har a kwai gaskiya a cikin bayanan kwamitin
binciken da gwamnatin shugaba Buhari ta sa a yi a kan kuxaxen makamai, har yau
xin nan ba wanda ya kama Janar Dambazau domin hukunta shi, uwa uba yanzu Janar
Dambazau yanzu minista ne a gwamnatin shugaba Buhari. Abubuwa biyu suka bayyana
daga wannan badaqala, na farko tun da Dambazau na cikin gwamnati zai iya hana
hukumomi masu bincike irin EFCC gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. A tuna fa
Janar Dambazau ya tava riqe muqamin ministan ma’aikatar harkokin ‘yan sandan Nijeriya
da kuma ta cikin gida. Na biyu lallai akwai alamun cewa gwamnatin shugaba
Buhari dodorido ce ko kuma angulu da kan zabo, domin bisa dukkan alamu ba
Buharin ne ke jan ragamar mulkin qasar nan ba, rahotanni da za a iya gani a
cikin jaridu da dama kamar ta Sahara Reporters ta watan Yuli 2016, ta ruwaito
wani xan siyasa Dakta Junaid Muhammad yana iqirarin cewa wasu ne ke mulki ba
Buhari ba. Cikin su kuwa akwai Mamman Daura wanda yake xan uwan shugaba Buhari
ne, shi kuma Mamman Daura shi ya reni Abba Kyari, wanda yake qusa ne a
gwamnatin shugaba Buhari. Akwai kuma cikin na hannun daman shugaba Buhari a
fadar Aso Rock, wanda shi ma suriki ne ga Mamman Daura. Haka kuma akwai wani
minista daga jihar Sakkwato da aka zavo da qarfi da yaji duk da al’ummar jihar sakkwaton
ba sa so, amma da yake xa ne ga qanwar Mamman Daura dole aka naxa shi kuma kowa
ya yi tsit. Haka Kuma an ga dogarin shugaba Buhari da ake kira kanar Abubakar
wanda yake auren jikanyar Buhari. Har wa yau ministan harkokin kuxi ita ma ‘yar
uwa ce ga Nasir El’Rufa’I, wanda shi ma ba sai an faxa ba na hannun daman
shugaba Buhari ne. Shi kuwa ministan harkokin babban birnin tarayya Abuja, ya
sami muqamin ne saboda babansa aminin Buharin ne na tsawon shekaru. Akwai wani
mai taimaka wa shugaba Buhari da ake kira Sabi’u Yusuf ko kuma Tunde, wanda shi
ma jika ne a wajen shugaba Buhari, kamar yadda Dakta Muhammed ya ruwaito.

Idan aka koma kan batun Hajiya Amina Zakari wadda ta
tava riqe shugabanci hukumar zave ta qasa, za a ga qazantar lamarin baki xaya.
Tun da farko dai Amina Zakari kwamishina ce a hukumar zaven ta qasa a zamanin
shugaba Jonathan, amma Buhari ne ya bada sunanta don wakilci yankin arewa maso
yamma, nan ma Buhari ya rasa wanda zai zava in ba ‘yar uwarsa ba daga duk
wannan faffaxan yanki. Wannan ne ya sa ko da aka naxa Amina Zakari ta kasance
mai kula da tattara da qididdige quri’un zaven 2019 ya sa mutane suka nuna
rashin goyon bayansu, domin ganin za ta iya yin amfani da wannan dama ta
taimaka wa xan uwanta a wajen zaven.

Daga xan abin da muka yi nazari za a ga munin irin
wannan abu da shugaba Buhari ke nema ya yi domin ba a tava ganin inda wani
shugaba ya zavi wani makusancin sa ba domin gudanar da zaven da shi kansa yana
cikin ‘yan takara ba, ba wannan kaxai ba, a halin da ake ciki qanin Amina
Zakarin shi ne ministan harkokin ruwa na Nijeriya duk a qarqashin mulkin
gwamnatin Buhari. Saboda haka daga waxannan misalai da ma wasu da ba a kawo ba
ta tabbata babu gwamnatin da aka tava yi da take yin naxe-naxe na manyan
muqamai ta hanyar rashin cancanta ko kuma ta amfani da ‘yan uwantaka kamar gwamnatin
shugaba Buhari. Ke nan babu abin da ya dace a halin yanzu sai ‘yan Nijeriya su
yi watsi da gwamnatin shugaba Buhari don kawar da wannan mumunan tsari na
gwamnatina da ta ‘yan uwana ko abokai, wanda in ba a yi hankali ba zai iya
jagwagwala lamurran mulki da ci gaban qasa da xabbaqa rashin adalci a tsakanin
al’umma.

Fidelis Nwagwu
ya rubuta daga Abuja

The post Me ya sa ake ganin cancantar Atiku Abubakar fiye da Buhari a zaben 2019? appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here