An Nada Farfesa Mele a Matsayin Shugaban Jami’ar Maiduguri
Jihar Borno – Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno ta nada sabon shugabanta.
An nada Farfesa Mohammed Laminu Mele a matsayin shugaban Jami’ar da ke Arewa maso Gabas.
An nada Farfesa Mele shugaban Jami’ar Maiduguri
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan Jami’ar, Ahmad Lawan ya fitar a jiya Laraba 18 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Tribune.
Sanarwar ta ce nadin zai fara aiki nan take inda ta ce an bi dukkan ka’idoji kafin nada Farfesan, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Read Also:
Ahmad Lawan ya ce Farfesa Mele ya cancanci wannan mukami saboda kwarewarsa.
Farfesa Mele dan asalin karamar hukumar Mafa ne a jihar Borno wanda ke da mata da kuma yara da dama.
Mele ya shefe shekaru 20 yana koyarwa da bincike da hidima ga al’umma domin cigabansu.
Maiduguri: Mukaman da Farfesa Mele ya rike
Kafin rike wannan mukami, Mele ya rike mukaddashin shugaban Jami’ar da kuma mataimakin shugabanta a bangaren gudanarwa.
Har ila yau, Farfesa Mele ya kasance kwararre a fannin yaren Turanci wanda ya shafe shekaru da dama a tsangayar koyar da harsuna.
Sanarwar ta taya Farfesa Mele murnar samun wannan matsayi mai daraja inda ta yi masa addu’ar fatan alheri da aiwatar da aikinsa cikin nasara.