Amma ashe wanzami ba ya son jarfa. Shi ya sa adalci hatta a magana yake da dadi. Da nan muka yi ta caccakar Jonathan komi kankantar abinda ya faru. Yau ta dawo kanmu sai so muke a yi shiru kar a ce komi. Don haka in ana cin baure, a bar tonon cikinsa.

To bakon da aka sallama dai yana bayan gari. Shi alhaki kuikuyo ne ai, mai shi yake bi. Sai a dage, don kar abinda ya ci doma, ya ci awai. Saboda dan hakin da ka rena, yana iya tsole maka ido.

Kuma a bar dukan kura da gwado. A ba yara makamai ingantattu. Da gizago ake sassaka, fartanya sai noma. Ko an ci kudin makamai ne don 2019 mu san cewa ko wace gauta ja ce?

In kunne ya ji, jiki ya tsira. Gyara kayanka ba sauke mu raba ba ne… Amma wanda ya ki jin bari ya ji hoho. A bar duk wata hayaniyar 2019 a mai da hankali a yakin nan. In ana ta kai ba a ta kaya. Ana ruwa ya ci makadi, mutum yana ganga ta jike.

 

The post Metele a idon Bahaushe – Aliyu Tilde appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here