Miji ya Kashe Matarsa Akan N1000 a Jahar Adamawa

Wani magidanci ya halaka matarsa saboda ta tambaye shi ya biya ta bashin N1000 da ya karba.

Rahotanni sun bayyana cewa magidancin mai shekaru 41 ya buga kan matarsa da bango ne kuma ta suma.

Yan uwan matar mai suna Rabiyatu Usman sun garzaya caji ofis sun yi wa yan sanda korafi kuma nan take aka kama mijin.

Jami’an yan sanda na jahar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.

Usman Hammawa, mazaunin yankin Jada a karamar hukumar Ganye ta jahar Adamawa, ya halaka matarsa ne ta hanyar buga kanta da bango, hakan yasa ta fadi sumammiya.

Kamar yadda rahoton na Daily Trust ya ce, an garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar ta riga mu gidan gaskiya.

‘Yan uwan matar suka yi korafi wurin yan sanda Yan sanda sun kama wanda ake zargin bayan yan uwan matar sun shigar da korafi a ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Ganye.

Usman, wanda ma’aikacin gwamnati ne a karamar hukumar Ganye, yana da yara biyar tare da marigayiyar bayan shekaru 16 da aure. Mai magana da yawun rundunar yan sandan ja

har Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, ya ce kwamishinan yan sandan jahar, CP Aliyu Adamu Alhaji, ya yabawa mazauna garin da yan sanda bisa tona asirin wanda ya aikata laifin domin ya girbi abin da ya shuka.

Amma, ya bada umurnin a gudanar da bincike ba tare da hayaniya ba domin a tabbatar wanda ake zargin ya fuskanci sakamakon laifinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here