An Mika Rahoton Karin Albashi a Kano

 

Jihar Kano – Abba Kabir Yusuf ya karbi rahoton kwamitin da ya kafa domin karin albashin ma’aikatan gwamnati.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa yana da tabbas a kan kwamitin zai yi aiki yadda ya kamata domin daidaita lamura.

Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa yadda aka mika rahoton a shafinsa na Facebook.

An mika rahoton karin albashi a Kano Shugaban kwamitin karin albashi a jihar Kano, Bala Usman ya mika rahoto bayan sun kammala aiki.

A yammacin yau Talata, 22 ga watan Oktoba kwamitin ya mika rahoto ga Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar Kano.

Yadda kwamitin albashi ya yi aiki a Kano

Wanda ya jagoranci kwamitin, Bala Usman ya bayyana cewa sun yi dubi ga tattalin arzikin Kano a yayin aikin.

Bala Usman ya kara da cewa sun yi adalci wa bangaren ma’aikata wajen ganin abin da za a biya su zai wadace su gudanar da rayuwar yau da kullum.

Yaushe Abba zai sanar da ƙarin albashi?

Abba Kabir Yusuf ya bukaci al’umma su kara hakuri wajen ba gwamnati lokaci ta yi nazari kan rahoton kwamitin.

Gwamnan ya bayyana cewa a mako mai zuwa zai sanar da kudin da gwamnatinsa za ta rika biya a matsayin mafi ƙarancin albashi.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here