Jirgin Kasa na Kaduna-Abuja: Minista Sadiya Umar Farouq ta Jajantawa Waɗanda Harin ya Rutsa da su
Ministan kula da Harkokin jin kai agajin gaggawa da inganta rayuwar al’umma, Sadiya Umar Farouq ta aika sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a cikin harin da aka kai wa jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna wanda wasu ‘yan bindiga suka kai wa hari a ranar Litinin a dajin Dutse da ke karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Ministan wadan ta bada umarnin gaggawar tura:
Ofishin NEMA Tawagar shiyyar Arewa maso yamma da su ziyarci wurin da aka farmaki jirgin kasan da kuma waɗanda abin ya shafa, sun bayyana lamarin a matsayin abin matukar ban tsoro.
Read Also:
“Ina miƙa saƙon ta’aziyata zuwa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai, Allah Ya basu juriyar rashin su Ya kuma Karfafe su a wannan lokacin bakin cikin. Ina kuma yi wa waɗanda suka jikkata dama waɗanda suke asibiti a kwance da waɗanda suka samu rauni addu’ar Allah ya basu lafiya”.
Bada jimawa ba, Tawagar Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa karkashin jagorancin ko’odinetan shiyyar, Abbani Imam Garki sun ziyarci waɗanda lamarin ya rista dasu mutum goma sha ɗaya dake karban kulawa a asibitin St. Gerald dake Kaduna. An mika majinyatan mutane takwas zuwa ga asibitin sojojin Najeriya 44 dake Kaduna, yayin da biyu daga cikin waɗanda suka samu raunukan harbin bindiga da karaya na kwance a asibiti.
Hukumar Asibitin ta tabbatar kan cewa sun karbi majinyatan mutane ashirin da biyar (25) wadanda suka samu raunuka daban-daban.
Wakilin Babban Jami’in Kula da Lafiya na 44 NARHK
Asibitin ta kuma bayyana cewa, yayin da aka yi wa wasu tiyata, an yi wa sauran waɗanda abin ya ritsa da su magani kuma ana lura da su cikin kulawa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna ta bukaci iyalan waɗanda lamarin ya shafa da su tuntubi 09088923398 domin jin karin bayani ko samar da bayanai akan fasinjojin da suka yi tafiya a jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022