Wani Ministan Buhari ya Shawarci Matasan Najeriya Kan Aikin yi
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya shawarci matasan Najeriya su nemi tayi domin samawa kansu aikin yi saboda gwamnati ba zata iya bai kowa aiki ba.
Ya yi gargadin cewa dogara kan gwamnati ba zai magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya ba.
Aregbesola ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan samawa mata da matasa aiki a yankin Osun ta tsakiya a jihar Osun.
Read Also:
A makonni biyu da suka gabata, ministan ya yi ganawa da kungiyoyi daban-daban a fadin jihar bisa ga umurnin shugaba Muhammadu Buhari bayan zanga-zangar #EndSARS da akayi a watan Oktoba.
Diraktan yada labaran ma’aikatar shiga da fice, Mohammed Manga, ya nakalto Aregbesola da cewa ayyukan gwamnati sun yi kadan idan aka hada da adadin daliban da ke kammala karatu kowace shekara.
Saboda haka, ya ce wajibi ne su nemawa kansu mafita domin samun kudi.
Ya ce ma’aikatar ta fara daukan mutane 5000 aikin hukumar NSCDC. Ya jaddada cewa mutane kadan kawai zasu samu shiga daga kowace karamar hukuma a fadin tarayya saboda yawan adadin marasa aikin yi.