Sababbin Hafsoshin Tsaro: Jawabin Ministan Kwadago da Ayyuka Kan Nadin da Shugaba Buhari ya yi
Sanata Chris Ngige, ministan kwadago da ayyuka ya taya Shugaba Buhari murna bisa nadin sabbin manyan hafsoshin sojoji.
Ngige ya bayyana sauyan manyan hafsoshin tsaron a matsayin goron sabon shekara da Buhari ya bawa yan Najeriya.
Ministan ya kuma ce yan kabilar Ibo sun yi murna domin nada Janar Leo Irabor wanda ya fito daga Niger Delta hakan kuma na nuna shugaban kasa baya kabilanci.
Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murna saboda nada sabbin manyan hafsoshin sojoji inda ya bayyana shi a matsayin “cika alkawari”, Premium Times ta ruwaito.
Read Also:
Sanarwar da ta fito daga sashin watsa labarai na Sanata Chris Ngige a Abuja ta ce nadin “goron sabuwar shekara ne ga ‘yan Najeriya’ kuma ya yaba wa shugaban kasar saboda sauraron kiraye-kirayen yan Najeriya.”
“Duk da cewa wasu ba su sani ba, shugaban kasa ya fada wa wasu tsirarun yan Najeriya cewa zai nada sabbin manyan hafsoshin tsaro a sabuwar shekarar. Ya cika alkawarinsa kuma babu shakka shugaba ne mai sauraron al’umma.”
Har wa yau sanarwar ta ce nadin ya yi wa yan kabilar Ibo dadi domin sabon shugaban hafsoshin tsaro, Janar Leo Irabor dan asalin karamar hukumar Ika ta Kudu ne daga jahar Delta kuma dan yankin Niger Delta don haka wannan alama ce da ke nuna shugaban kasar baya nuna kabilanci.
“Nadin ya nuna karara cewa shugaban kasa yana la’akari da cancanta ne kuma ya kan zabo tawagarsa daga bisa cancanta daga kowanne yanki na kasar.”