Ministan Kwadago ya yi Martani Kan Yajin Aikin ASUU
Minista kwadago ya bayyanawa yan Najeriya shi mai kishin kasa ne.
Ya ce har wasu mambobin kungiyar ASUU ya fi kishi saboda makarantun kudi suka sanya yaransu ba na gwamnati.
Ministan kwadago da daukan aiki, Chris Ngige, ya lashi takobin tabbatar da cewa kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU bata sake zuwa yajin aiki ba.
Ministan wanda ya lashi takobin haka a hirarsa da tashar Channel TV ranar Laraba, 23 ga Nuwamba, ta ce yaransa uku na gida kuma yajin aikin ya shafesu.
Read Also:
Ya kara da cewa biyu cikin wadannan yaran nasa a Amurka aka haifesu kuma yana da daman kaisu can suyi karatu kyauta, amma bai yi hakan ba.
Ngige yace: “Ba san sake baiwa ASUU daman zuwa yajin aiki. Saboda ina da yaran cikina uku da suka wahala da wannan halin da muka samu kanmu ciki harda da kuma yara 15 da nike daukar nauyinsu a jami’o’in Najeriya.”
“Ina da yara uku dake karatu a jami’o’in Najeriya. Ko sakandare a nan sukayi. Biyu cikinsu haifaffun Amurka ne kuma ina da daman kaisu Amurka karatu kuma kyauta ma, amma ban yi haka ba.”
“Saboda haka ni mahaifi ne na kwarai, da ni ake damawa, kai na fi wasu mambobin ASUU kishi saboda ‘yayansu makarantun kudi suke zuwa.”