Kungiyar Miyetti Allah Zata Horar da Makiyaya Yadda Ake Kiwon Zamani

 

Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana yunkurin horar da makiyaya yadda ake kiwon zamani.

Wannan na zuwa ne daga bakin jakadiyar kungiyar, Amina Ajayi wacce ta halarci wani taro.

A cewar Ajayi, shirin horarwar zai taimakawa Fulani makiyaya su kware a fannin kiwo na zamani.

Nassarawa – Amina Ajayi, Jakadiyar Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hure, kungiyar raya al’adu, ta gabatar da wani shiri mai karfi na horar da Fulani makiyaya akan kiwo na zamani, wanda aka misalta shi da kwatankwacin kiwo a Amurka.

Ajayi ta bayyana hakan ne a cikin jawabinta na karbar mukami biyo bayan nada ta a matsayin Jakadiyar Miyetti Allah a hedikwatar kungiyar ta kasa da ke Uke, Karamar Hukumar Karu ta Jahar Nasarawa.

Ta bayyana cewa rukunin farko na masu horaswa da malamai na makarantar Miyetti Allah Cattle Ranch Academy zai yi tafiya zuwa California a kasar Amurka, a farkon 2022, Vanguard ta rawaito.

A cewarta:

“Duk da haka, kafin karshen shekarar 2021, ofishina, a karkashin kulawar Shugaban Miyetti Allah, zai shirya wani shirin horaswa na gida a Najeriya don tantancewa da daukar rukunin farko na masu horarwa da malaman da za su je Silicon Valley, California, don horon kasashen waje.

“Babban makasudin shirin shine a horar da su fasahohin zamani kuma ingantattu a fannin kiwo, wuraren kiwo da kiwo a kebabben wuri.

“Kamfanin mu na Silicon Valley Nigeria Development Development (SV-NED Inc) ya kammala dukkan shirye-shirye tare da abokan aikin mu a California, Amurka.”

Za a ginawa makiyaya gidaje miliyan daya

Jakadiyar ta kuma bayyana cewa kashi na biyu na shirin ta shine gina gidaje masu rahusa miliyan daya ga Fulani makiyaya miliyan daya da ke manne da gidajen gonarsu.

Ta ce kamfanin nata ya hada gwiwa da Bankin Gidaje na Tarayya kan tsarin gidaje, ta kara da cewa shirin zai canza fuskar kasuwancin kiwo da daidaita shi da mafi kyawun ayyuka na duniya.

Tun da farko, Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello Bodejo, ya yi kira ga majalisar kasa da ta kawo agaji ga makiyaya ta hanyar farfadowa da zartar da dokar Hukumar Kula da Kiwo.

Bodejo ya kuma yabawa hukumomin tsaro kan sabon kokarin da suke yi na dakile satar shanu, garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran ayyukan ta’addanci a kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here