Jihar Montana a Amurka za ta Haramta Amfani da Manhajar TikTok
Jihar Montana ta kasance ta farko a Amurka da ta amince da ƙudurin dokar haramta amfani da manhajar Tiktok.
Idan har gwamnan jihar ya sanya hannu kan ƙudurin dokar to babu shakka amfani da Tiktok zai zama wani laifi.
Read Also:
Wannan gagarumin matakin na haramta Tiktok a hukumance da wata jiha ta yi saboda dalilai na tsaro ya zo ne a daidai lokacin da wasu jihohin na Amurkar ke tattaunawa batun.
Tiktok dai ya sha musanta zargin da ake masa na ba da bayanai ga gwamnatin kwaminisanci ta China ta hanyar miƙa bayanan sirri na masu amfani da shafin ga hukumomin Beijing.
A ƙarƙashin dokar, dole Apple da Google su cire manhajar ta Tiktok daga rumbun sauke manhajojinsu.
Tuni dai ƙasashen Amurka da Canada da kuma wasu na Turai suka haramta amfani da Tiktok a wayoyi da kuma kwamfutocin gwamnati.