Gano ‘Yan Ta’adda: Rundunar Sojojin Najeriya ta Kirkiro Motoci Masu Hangen Nesa
Rundunar sojojin Najeriya ta kirkiro wasu motoci masu hangen nesa don gano ‘yan ta’adda.
Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro suke kara lalacewa a yakuna daban-daban na Najeriya.
An samar da motocin masu kymarori a jikinsu da kan iya hango abubuwa daga nisan kilomita 6.5 .
Babban hafsan sojojin kasa (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, a ranar Litinin 13 ga watan Satumba, ya ba da sabbin motocin sadarwa na tauraron dan adam wadanda za a tura su ga rundunoni daban-daban na sojoji a fadin kasar.
Read Also:
Motocin na dauke da kyamarori da kayan aikin lantarki na zamani, kuma rundunar sojan Najeriya ta Cyber Warfare Command, Abuja ta kirkiresu, The Sun ta rawaito.
Da yake jagorantar COAS yayin ziyarar duba motocin, Kwamandan, Cyber Warfare Command, Birgediya Janar Adamu, ya ce motocin na hango abu daga nisan kilomita 6.5 kuma an sanya masu na’urorin da za su taimaka a hango abubuwa ko da cikin dare ne.
Adamu ya kuma ce motocin na iya jujjuya na digiri 360 kuma suna da irken intanet don baiwa sojoji damar yin kira zuwa cibiyoyin aiki, ofishin COAS, cibiyar yaki ta yanar gizo da kuma sanya ido kan duk ayyukan sojoji a kasar.
Ya ci gaba da bayyana cewa motocin, wadanda kuma ke aiki a matsayin cibiyoyi masu iko da sarrafawa, za su ba kwamandoji damar sauke bayanai a wayar su ta hannu da aikawa zuwa ga sauran kwamandojin.