Batanci ga Addini: Maganganun Malamai kan Hukuncin da Kotu ta Yankewa Mubarak Bala

Guda cikin malaman Addinin islama Sheik Malam Aminu Abubakar mai Diwani ya yaba da hukuncin da babbar kotun jihar Kano ta yanke kan Mubarak Bala.

Inda yace abu ne da dukkanin masoyin Manzon (S.A.W) zai yi farin ciki duk da ba’a yanke hukunci a bisa tsarin da addinin ya tanadar ba.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da jaridar Arewa Agenda, a yammacin ranar talata.

Yace ;

“Hakika wannan kotu data yanke hukunci kan Mubarak Bala ta tura shi gidan gyaran hali shekara 24, wannan abin farin ciki ne ga dukkan musulmi kuma haka ya kamata a dinga yiwa masu yin katobara a janibin Ma’aiki”

“Duk musulmi na kirki kololuwarsa lamarin Allah da Manzon Allah, saboda haka wannan hukunci yayi daidai, domin irin wannan dabi’a da wasu cikin mutane ke aikatawa ko da a kasashen da ba su san addini ba, ba za ayi hakan ba.

Ya kara da cewa a shari’ar musulunci dukkan wanda ya taba mutuncin Annabi koda ya tuba bai kamata a kyale shi ya tafi haka ba, ya cancanci hukunci mai tsaurin gaske.

“Bai kamata jiha ta musulunci irin Kano ace wannan katobara ta dinga zuwa ba, Shi Manzon Allah (SAW) mutuncin sa duk wanda ya taba ba’a barin sa, ba wai hukunci bane na shekaru 24 da kotun ta yake masa ba, da doran shari’a za’a bi, wanda ya taba kima da martabar Manzon Allah hukuncin kisa ya hau kan sa.

A cewar Malam Aminu Mai Diwani.

Mai Diwani ya kara da cewa wannan hukunci zai zama kamar tauna tsakuwa ne domin Aya taji tsoro.

“muna goyon baya mutum ko daga wacce kungiyar addinin ya fito, babu maganar wane dan waccen kungiya ne, ko wane dan waccen Da’ifa duk wanda ya taba daraja ta Annabi a isar masa da sakon doka ta Allah”

“amma idan abin yakai ga anata yawo da hankulan mutane to gara aje a rufe mutum har abada, duk da dai ba wannan ne abinda muke nema tun da farko ba”

Shima Babban Limamin Masallacin Juma’a na Mal. Muhammad Khamis dake garin gwagwarwa a jihar Kano, sheik Auwal Alhassan Gwagwarwa, yace;

sanin kowa ne Manzon Allah S.A.W shine Annabin da Allah ya aiko shi ga dukkan Al’ummar musulmi kamar yadda Musulmin suka yi Imani.

“Don haka girman Manzon Allah S.A.W ya wuce baki ya iya fadin sa, ballenta takai aibata shi, don haka dukkan wanda ya zage Shi hukunci sa shine kisa, ko mutm ya aibata Shi, ko ya zageshi ko kuma kabi ta ko wacce irin hanya wadda zaka kawo nakasu a gareshi kuma to wannan hukuncin ya haukanka”.

Daga bisani shaihin malamin ya bukaci Al’ummar musulmi da suyi takatsantsan wajen yin kalami ga Janibin Annabi S.A.W.

Idan dai za’a iya tun a watan Afrilun 2020 ne aka zargi Mubarak Bala da cin zarafin addinin Musulunci a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wata tawagar lauyoyi ta miƙa wa ‘yan sanda ƙorafi a Jihar Kano inda su kuma ƴan sandan Jihar Kaduna suka kama Mubarak Bala suka mayar da shi Kano jiharsa ta haihuwa, inda a can ne dimbin Musulmai suka rubutawa hukumomi korafi da zarginsa da yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

A lokacin wasu masu rajin kare hakki sun yi ca a shafukansu na zumunta suna neman a saki Mubarak Bala, wadanda suka ce yana da ‘yancin shiga addinin da ya kwanta masa a rai.

Barista Salisu Salisu Umar ne jagoran lauyoyin da suka yi ƙorafi kan Mubarak, kuma tun farko ya faɗa wa BBChausa cewa ba don ya bar addinin Musulunci suka nemi a kama shi ba.

“Mun yi musu ƙorafi ne kan aibata Annabi S.A.W. da ya yi a shafinsa na Facebook,” a cewar Salisu Salisu.

Ya ci gaba da cewa:

“Ba wai don ya yi ridda ba ne ko sabo, korafinmu a kan barin masu addini su yi addini ne.”

“Abin da muke nufi shi ne, tun da shi (Mubarak Bala) ya bar Musulunci tun a shekarar 2014 bai kamata kuma ya rika aibata addinin ba da kuma abin da masu binsa suka yi imani da shi.

“A matsayinmu na lauyoyi, daga cikin hakkinmu mun nemi ‘yan sanda su binciki abin da yake fada ko ya saba da abin da aka iyakancewa mutum ya yi magana kan addini.”

Barista Salisu ya bayyana cewa suna so ne a hukunta shi da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Mubarak Bala shi ne shugaban wadanda babu ruwansu da addini a Najeriya wato Humainists Asociation of Nigeria.

A shekarar 2014 ne matashi Mubarak Bala mai shekara 29, a lokacin, da ya ke birnin Kano ya ce bai yarda da samuwar Allah ba kuma ya ce ya bar addinin Musulunci.

Iyayensa sun kai shi asibitin masu tabin hankali domin binciken lafiyarsa a lokacin.

Sai dai ya samu ya riƙa yada halin da ya shiga ga duniya ta shafinsa na twitter ta hanyar amfani da wata waya da aka kai masa a sace a asibitin.

Abin da ya ja hankalin wata kungiya mai da’awar kare hakkin wadanda ba su da addini mai suna International Humanist and Ethical Union, wadda ta shiga kiran a sake shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here