Muhimman Abubuwa 6 a Kan Sabon Hafsin Sojoji, Janar Farouk Yahaya

 

Farouk Yahaya sojan Najerya mai mukamin Manjo Janar wanda ya fito daga jahar Sokoto dake arewa maso yammacin kasar nan.

Sabon shugaban hafsin sojin Najeriyan ya halarci makarantar horar da hafsin sojoji inda ya kammala a aji na 37.

Kafin nadinsa, shine mai baiwa rundunar Operation Hadin Kai umarni dake yankin arewa maso gabas.

A yau 27 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Yahaya Farouk a matsayin shugaban hafsin sojojin kasa na Najeriya.

Idan zamu tuna, tsohon shugaban hafsin sojojin kasa, Marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru ya rasu sakamakon hatsarin jrigin sama tare da wasu jami’ai 10 a ranar Juma’a 21 ga watan Mayu.

An birnesu bayan jana’izar da aka yi musu a ranar Asabar 22 ga watan Mayu a Abuja inda wasu ministoci da gwamnoni suka samu damar hallara.

Nadin Farouk Yahaya ya bazu ne bayan sanarwar da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafin hedkwatar na Twitter.

Ga muhimman abubuwa shida da ya dace a sani game da sabon shugaban dakarun sojojin kasan:

1. Har zuwa yau da aka nada shi, Manjo janar Farouk Yahaya shine mai bada umarni ga rundunar Operation Hadin Kai wacce a da aka sani da Operation lafiya Dole a yankin arewa maso gabas.

2. Sabon shugaban hafsin sojojin kasan dan asalin jahar Sokoto ne.

3. Yahaya ya halarci makarantar horar da hafsin soja dake Kaduna kuma ya kammala a aji na 37.

4. Shine tsohon babban jami’i mai bada umarni ga Div 1 dake rundunar sojin Najeriya.

5. Sabon shugaban hafsin sojojin kasan ya karba ragamar cibiyar bincike ta rundunar sojojin kasa daga hannun Manjo Janar Olusegun Adeniyi.

6. Shine mai bada umarni ga birged ta hudu ta rundunar sojojin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here