Muhimmancin Dacewa da Daren Lailatul Qadri – Dr Kabir Asgar

 

Mabiya addinin Islama na cikin kwanaki goma na karshe a watan Ramadana.

Malaman addinin sun kwadaitar da mabiyansu da su dukufa cikin Ibada a wadannan kwanaki.

A hira da wani babban Malami, ya yi bayani kan muhimmancin dacewa da daren Lailatul Qadri.

Musulmai a fadin duniya a cikin kwanakin goma na karshe na wata mai alfarma ta Ramadana na gudanar da ayyukan Ibada domin dacewa da daren Lailatul-Qadri.

Domin sanin dalilin haka, Legit.ng ta tuntubi babban Malami, Dr Kabir Asgar, domin bayani kan muhimmancin wannan dare da kuma yadda aka gane an dace da daren.

Dr Kabir Asgar ya bayyana cewa Allah ya bayyana cikin Al-Qur’ani mai girma cewa wannan dare da Musulmai ke nema ya fi watanni 1000.

A bayanin Malamin, bautan Allah cikin daren tamkar bauta cikin watanni 1000 ne da kuma ladan da za’a samu a cikinsa.

“Daren Lailatul Qadri dare ne mai daraja kwarai da gaske, wanda Allah SWT yake cewa wannan dare darajarsa daya da wata dubu,” Malamin yace.

“Ana iya samun daren ya dace da ranar 21, ko 23, ko 25, ko 27 ko 29. Dalilai suna karfafa ya fi zuwa a 27 fiye da sauran dararen.”

“Dare ne wanda idan mutum ya dace da shi yana ibada, kamar ya yi dare dubu ne yana ibada.”

Game da yadda mutum zai gane ko ya dace da dare, Dr Asgar ya ce akwai alamu da suka tabbata daga Manzon Allah kan alamun daren.

“Mutum zai iya ganewa, akwai alamu da ake iya ganewa. Za’a tarar da dare ne mai natsuwa, za aji wata natsuwa ta musamman wanda ya sabawa sauran dararrakun,” yace.

“Sannan kuma idan gari ya waye, za’aga cewa rana ta fito amma ba tada zafi, sai dai haskenta amma ba zafi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here