Buba Galadima Zuwa Buhari: Mulkin Damokradiyya Muke ba na Sojoji ba
Buba Galadima ya yi Allah-wadai da daskarar da asusun bankunan wasu jagororin zanga zangar EndSARS da gwamnati ta yi.
Gladima ya tunatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa a mulkin damokradiyya ake ba na sojoji ba.
Ya ce sam gwamnati bata da yancin daukar wannan mataki a kan masu zanga zangar Buba Galadima, tsohon aminin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi watsi da takunkumin da aka sanya wa wasu masu zanga zangar EndSARS.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya samu wani umurnin kotu, inda ta umurci wasu bankuna da su daskarar da asusun mutane 19 da wani kamfani da ka alakanta da zanga zangar EndSARS kan zargin daukar nauyin ta’addanci.
Modupe Odele, wata mai kare hakkin dan adam wacce ta taimakawa mutanen da aka kama a yayin zanga zangar, ta ce hukumar kula da shige da fice ta kwace mata fasfot dinta.
Read Also:
Da yake magana a lokacin da ya bayyana a shirin Arise TV a ranar Litinin, Galadima ya bukaci Buhari da ya yi umurnin bude asusun bankunan da aka daskarar.
Galadima ya bayyana yunkurin a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki, sannan ya tunatar da Shugaban kasar cewa Najeriya na mulkin damokradiyya ne ban a sojoji ba.
”Abunda gwamnati ta yi ba daidai bane. Bata da ikon hana yan Najeriya tafiya zuwa wajen kasar ko kuma hana su iko da asusun bankunansu. Daskararwa kan wani dalili? Me suka yi?” Galadima ya tambaya.
“Wadannan matasa sun yi zanga zangar lumana ne a kan hukumomin gwamnati. Me yasa bayan kun lallashe su ko bayan jami’an gwamnati sun far masu ko kashe su, sannan kuka dauki wannan mataki na toshe asusun bankunansu? Wannan baya bisa kundin tsarin mulki.
“Ina aika wannan sakon zuwa ga shugaban kasa imma ya sani ko bai sani ba, a nuna masa abunda na fadi.Mutanensa basu da hakkin yin abunda suke yi.
“Dan Allah su janye sannan su bude asusun wadannan matasa sannan su barsu su gudanar da harkokinsu a matsayinsu na yan Najeriya. Ba za ku iya razana su ba. Muna mulkin damokradiyya ne ba na sojoji ba.