Wani Gwamnan APC Zai Marawa Matasan Jaharsa Baya Akan Zanga-Zangar Endsars

Ni kaina na fuskanci cutarwa a hannun ‘yan sanda a 2014, cewar gwamnan jihar Ekiti, Dr Fayemi Kayode.

A cewarsa, lokacin da suke yakin neman zabe, saboda tsananin cutarwa, daya daga cikin jiga-jigan APC, Taiwo Akinsola, ya rasu.

Kayode ya ce zai cigaba da mara wa matasan jiharsa masu kyawun niyya baya, don dakatar da zaluncin ‘yan sanda.

A Jiya ne gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi ya bayar da labarin irin bakar wahalar da ya fuskanta a hannun ‘yan sanda, inda yace yana daga cikin wadanda ‘yan sanda suka cutar a 2014.

Gwamnan ya ce wasu daga cikin ‘yan sandan, sun taimaka masa kwarai, a cewarsa, wasu ‘yan sanda sun jefa masa barkonon tsohuwa yayin yakin neman zaben takarar gwamnan jihar a 2014.

Bayan ‘yan jam’iyyar PDP sun gama rali, jam’iyyar APC ma ta fara nata, inda Fayemi da masu mara masa baya su ka bi titina suna shara, kawai sai rundunar ‘yan sanda ta afka musu,.Garin hakan har wani shugaban APC, Taiwo Akinsola, ya rasa ransa.

Gwamnan ya fadi hakan ne a wata hira da aka yi da masu fadi a ji a kan zanga-zangar EndSARS wacce ta karade kasar, inda Fayemi yace zai cigaba da yin kira a kan dakatar da mugayen ‘yan sanda, shi da masu kyakkyawar niyya a cikin masu zanga-zangar.

Ya ce muguntar da ‘yan sanda suke yi tana daya daga cikin manyan matsalolin da al’umma take fuskanta, ThisDay ta wallafa.

Yace a jihar Ekiti, sun yi na’am da zanga-zangar, saboda kyakkyawan makasudin ta. Matasan jihar Ekiti sun yi zanga-zangar da kyakkyawar niyya kuma cikin lumana. A cewarsa a karo na farko kenan da majalisar zartarwa tayi gaggawar amsar korafi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here