Jam’iyyar PDP ce Kadai zata Iya yi wa Kowa Adalci a Najeriya – Atiku Abubakar

 

Najeriya ba ta da babban abokin da ya wuce Jam’iyyar PDP, cewar Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fadi hakan ne a Twitter.

Ya ce PDP ce kadai jam’iyyar da za ta iya yi wa kowa adalci a Najeriya Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya ce PDP ce babban abokin Najeriya.

Atiku ya ce PDP ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16 kafin APC ta amshi mulkin Najeriya a 2015, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Atiku ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, inda yace, “PDP ce babban abokin Najeriya.

Duk bangarorin Najeriya suna bukatar jam’iyyar da za ta gyara Najeriya, ba wacce za ta lalata ta ba.

“Jam’iyyar PDP ta tabbatar da za ta gyara Najeriya, sannan ina rokon ‘yan Najeriya da su amince da jam’iyyar don za ta tabbatar da adalci ga kowa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here