Tsohon Gwamnan  Nasarawa, Abdullahi Adamu ya Bayyana Mulkin Karba-Karba a Matsayin Wanda ya Saɓawa Kundin Tsarin Mulki

 

Sanata Abdullahi Adamu na jahar Nasarawa ya ayyana cewa tsarin karba-karba ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya

Tsohon gwamnan, wanda ya bayyana haka a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, ya ce za a yi amfani da cancanta don zaɓar ɗan takarar jam’iyyar.

Adamu ya kuma lura cewa abin fata ne ga mutanen kudu su so fito da wanda zai maye gurbin Shugaba Buhari a 2023.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jahar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gaya wa wadanda ke kira ga mika shugabanci zuwa yankin kudancin ƙasar a 2023 da su binne tunaninsu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Adamu wanda shine sanata mai wakiltar yankin Nasarawa ta yamma a majalisar tarayya ya bayyana mulkin karba-karba a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulki.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon gwamnan na sau biyu ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa tsohon gwamnan na Nasarawa ya ce duk da cewa akwai kiraye-kirayen da ake yi na mika kujarer shugaban kasa ga shiyyar kudu maso gabas, amma babu wani tanadi na tsarin mulki kan hakan.

A cewarsa, tunda ra’ayin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulkin kasar, kowane dan Najeriya da ya cancanta yana da ‘yancin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba tare da la’akari da jaharsa ta asali ba.

Ya ce:

“Babu wani wuri a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da aka ce mu raba kowani kujerar gwamnati zuwa wani yanki. Akwai halin tarayya. Amma ba wai dole ne jam’iyyu su mika mukamin shugaban kasa ga wani yanki ba a lokacin zaɓe.

“Ana nazarin kundin tsarin mulki. Idan kuna son takamaiman tanadi cewa a karkatar da mukaman shugaban ƙasa zuwa na karba-karba, sai ku faɗi – sannan ku gaya mana yadda kuke son a raba shi.

“Shin zai kasance daga wannan shiyya zuwa wani ne? Ba za ku iya yin fatan kawai ba, a yanayin da ke da mahimmanci ga ƙasa. Ba za ku iya yin magana game da cancanta da magana kan karba-karba ba. Ba za ku iya ba.”

“Na yarda kuma ina tausaya musu amma tsarin mulki ya ce za ka iya zama shugaban kasa ne ta akwatin zabe kawai. Mun kasance muna fada a lokacin zabe cewa dole ne a kirga kowane kuri’a. Don haka, me yasa kuke son yin karba-karba?”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here