Mummunan Hasashe Game da Najeriya ba Zai Cika ba – Lai Mohammed

Lai Mohammed ya bayyana cewa Najeriya ba zata taba zama kasar da zata gaza ba.

Ya kuma jaddada cewa kasar na da samun ci gaba wajen yaki da ‘yan fashi da barayi.

A kalubalen da ya yi wa wata jaridar waje, ya bayyana ci gaba da aka samu na tsaro a wadannan shekaru.

Gwamnatin Tarayya ta fada a ranar Litinin cewa Najeriya ba ta gaza ba kuma ba za ta taba gazawa ba.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Legas.

Financial Times ta Landan a ranar 22 ga watan Disambar da ta gabata ta gabatar cewa Najeriya na cikin hatsarin zama kasar da ta gaza sakamakon lamuran sace-sace da ‘yan fashi.

Amma Ministan ya kalubalanci babbar jaridar kasuwanci, yana mai cewa Najeriya “ba za ta iya zama kasar da ta gaza ba.”

A cewar Mohammed, Najeriya na samun ci gaba matuka wajen magance barayi da satar mutane.

Ya jaddada cewa hasashen mummunan abu game da Najeriya ba zai cika ba, yana mai tuna cewa wasu masu sharhi na karya sun yi hasashen cewa Najeriya za ta shiga cikin shekaru 20 da suka gabata.

“Wannan bai faru ba kuma ba zai faru ba,” in ji shi, ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta samu ci gaba sosai wajen magance rashin tsaro kamar yadda ake gani tare da bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara cikin lumana.

Ya tunatar da cewa a shekarar 2010 da 2011, hare-haren bama-bamai na Kirsimeti da sabuwar shekara sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkata da dama amma yanzu ba haka batun yake ba, yana mai bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da yaki da ta’addanci da satar mutane.

Mohammed ya bayyana shekarar 2020 a matsayin shekara mai matukar kalubale saboda annobar COVID-19, da zanga-zangar #EndSARS da kuma “tsananin rashin tsaro.”

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa kasar za ta samu ci gaba mai kyau a shekarar 2021 kuma ta fita daga matsin tattalin arzikin da take ciki a yanzu ta hanyar ayyukan gwamnati da dama a bangarori da dama na tattalin arziki.

“Mummunan Hasashe game da Najeriya ba zai cika ba. Najeriya ba za ta zama kasar da ta gaza ba, amma za ta tashi ne don zama kasar da ake girmamawa a cikin wasu kasashe,” in ji shi

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here