Sanata Giwa: Mun Gaza, ku Yafe Mana#ENDSARS
Sanata Florence Ita-Giwa ta gurfana a kan guiwoyinta tana rokon fusatattun matasa a Calabar
Read Also:
Kamar yadda bidiyon ya bayyana, ta amince da cewa shugabanni a Najeriya sun gaza Ta bukaci matasan da su dauka hakuri a kan abinda ke faruwa a kasarsu, su daina rikicin Tsohuwar mai bada shawara ta musamman a kan al’amuran majalisar dattawa, Sanata Florence Ita-Giwa, ta gurfana a kan guiwoyinta inda take rokon matasa da su daina kwashe musu kadarori a Calabar. Ta yi wannan kiran ne a ranar Asabar, inda ta amince da cewa shugabannin sun gaza kuma sun ci amanar matasa, Channels TV ta wallafa. Kamar yadda tsohuwar sanatar ta sanar, lalata kadarori tare da haddasa rikici da ake yi yanzu kawai yana shafar masu kudi ne amma talakawa suna rayuwarsu lafiya kalau.
“Ina rokon ku ‘ya’yana, mun san cewa mun gaza kuma mun yi kuskure. Kasar ku Najeriya ta gaza kuma shugabannin sun kasa tsayar da wannan rikicin,” tace. A tun farko, gwamnan jihar Farfesa Ben Ayade ya saka dokar ta baci na sa’o’i 24 domin dakile rikicin da ya hada da wasu sasaan jihar. Kamar yadda takardar da ta fita a ranar Juma’a ta nuna cewa dokar ta bacin za ta fara ne a take. Wannan cigaban kamar yadda takardar ta bayyana, an tabbatar da ita ne domin rikicin da zanga-zangar ta koma a fadin jihar. A yayin bai wa jama’ar jihar shawara, Ita ta ja kunnen jami’an tsaron da su damke duk wanda ya take dokar.