Kungiyar MURIC da CAN Suna Fafatawa Akan Shugabancin 2023

 

Ga dukkan alamu fafatawa da ake yi game da shugabancin 2023 ya ɗauki salon addini tsakanin MURIC da CAN.

Kungiyar Musuluncin ta mayar da martani kan sanarwar baya bayan nan da Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta fitar.

Kungiyar Kiristocin a baya ta dage kan cewa dan kirista ne ya kamata ya zama shugaban Najeriya na gaba .

Lagos – Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi (MURIC), ta mayar da martani kan sanarwar da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta fitar kwanan nan inda ta yi kira ga shugaban kasa dan Kirista a 2023.

MURIC ta ce ita bata adawa da samar da shugaban Najeriya kirista, amma cewa dole ne CAN ta jira zagayen ta, jaridar Daily Post ta ruwaito.

Darakta kuma wanda ya kafa MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana matsayin kungiyar a ranar Litinin, 2 ga Agusta a cikin wata sanarwa.

Sashin bayanin ya zo kamar haka:

“Cif Mathew Aremu Olusegun Obasanjo, Kirista, ya kwashe shekaru takwas yana shugabantar kasa. Dr. Goodluck Ebele Jonathan shima ya kwashe shekaru biyar. Wannan ya kawo jimlar da shugabannin Kiristoci suka kashe a Aso Rock zuwa shekaru goma sha uku.

“Musulmai za su ragu a shekaru biyu ko hudu idan Kirista ya zama shugaban kasa a 2023. Abin da ya fi dacewa shi ne a bar wani Musulmi ya yi wa’adi daya kacal daga 2023 zuwa 2027.”

Kungiyar ta shawarci CAN da ta jira lokacin ta sannan ta kara da cewa ya kamata kungiyar Kiristocin ta daina rura wuta a yanayin siyasa da bukatu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here