Yadda Taron ASUU da Gwamnatin Tarayya ya Kasance

Gwamnatin tarayya ta nuna gamsuwarta game da taron da ya gudana tsakaninta da ASUU.

Ministan kwadugo, Chris Ngige, ya bayyana taron na su a matsayin wanda aka ci nasara.

Shugaban ASUU ta kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, yace zasu yi taro da sauran mambobinsu domin duba abun yi FCT.

Abuja:- Gwamnatin tarayya ta bayyana taron ta da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) domin duba yarjejeniyar gudanarwa (MoA) a matsayin wanda aka samu nasara, kamar yadda leadership ta ruwaito. Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, ministan kwadugo, Chris Ngige, yace taron ya tattauna muhimman abubuwa 7.

Ministan ya bayyana cewa kowane ɓangare ya nuna gamsuwarsa da matakin aiwatarwa da ake ciki yanzun haka.

Yace wasu daga cikin abubuwan da aka amince da su a MoA kusan an kammala aiwatar da su kashi dari bisa ɗari.

Shin an aiwatar da tsarin biyan albashi na UTAS?

Ministan ya kara da cewa an umarci hukumar NITDA da ta gudanar da bincike kan sabon tsarin biyan albashi na UTAS da kungiyar ASUU ta gabatar.

Wanda a cewarsa idan aka samu nasara zai magance ƙalubalen da malaman ke fuskanta a ɓangaren biyan su albashinsu.

Dakta Ngige yace gwamnati ta riga ta fitad da kuɗi biliyan N30bn na farfado da jami’o’i kamar yadda aka amince a MoA tun a watan Janairu.

Channels tv ta ruwaito ministan na cewa:

“A halin yanzun kuɗin na babban bankin Najeriya (CBN) yayin da ake jiran kammala rahoto binciki na kwamitin gudanarwa dangane da kuɗin da aka fitar a baya.”

“Bayan kuɗin alawus biliyan N40bn da gwamnati ta biya, yanzun an saka alawus ɗin malaman na 2021 kimanin biliyan N22bn a cikin karin kasafin kudi kuma ba da jimawa ba za’a sake su.”

Wane mataki ASUU zata ɗauka?

A bangaresa, shugaban ASUU na ƙasa, farfesa Emmanuel Osodeke, ya nuna gamsuwarsa game da abinda taron ya kunsa.

Sannan ya yi alkawarin kai dukkan sakamakon taron gaban mambobin kungiyar domin yanke hukunci.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here