Ta’addanci: MURIC ta yi Martani Kan Ikirarin da CAN ta yi na Cewa an fi Kashe Kiristoci

 

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta karyata ikirarin da kungiyar Kiristoci CAN ta yi na cewa kiristoci ne yan ta’adda suke kashewa kadai saboda addininsu.

Farfesa Ishaq Akintola, shugaban MURIC ya ce hasali ma musulmi yan ta’addan suka fi kashewa domin hare-haren sun fi yawa a arewa kuma musulmi ke da rinjaye a arewan.

Akintola ya ce kawai su al’ummar musulmi suna birne gawarwakinsu cikin gaggawa ne ko da yan ta’adda sun kai musu hari amma kiristoci na ajiye gawa na kwanaki ko watanni kuma suna nuna gawar a wurin jana’iza a yi ta daukan hotuna.

Jihar Legas – Kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta dage cewar ikirarin da shugabannin kirista ke yi na cewa kiristoci kadai ake kashewa a Najeriya ba gaskiya bane, Daily Trust ta rahoto.

Hakan martani ne kan sanarwar da sanatocin Amurka biyar, Josh Hawley, Marco Rubio, Mike Braun, James Inhofe da Tom Cotton wanda suka tura wa sakataren Amurka wasika mai kwanan watan ranar 29 ga watan Yunin 2022 suna ikirarin cewa “nuna cewa mutum kirista ne tamkar hukuncin kisa ne a sassan Najeriya da dama.”

Sanatocin na Amurka sun fitar da sanarwar ne bayan takardar korafi da shugaban kungiyar kiristoci na Najeriya, CAN, ta rubuta na zargin cewa ana musgunawa kirista a kasar.

Martanin MURIC

A yayin jawabin wurin taron manema labarai a ranar Alhamis a Legas, shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce an fi kashe musulmi tun farkon ta’addancin a Najeriya.

Ya ce a yayin da sanatocin na Amurka suka yi ikirarin cewa an kashe kirista 4000 a Najeriya zuwa shekarar 2021, duk da cewa yana tantama kan alkalluman, Akintola ya ce sunyi watsi da fiye da musulmi 40000 da aka kashe a wannan lokacin.

A cewar Ishaq, shugabannin kiristocin kawai suna amfani da kallubalen tsaro da kasar ke fama da shi ne a yanzu.

“Gaskiya shine kashi 90 cikin 100 na wadanda Boko Haram da ISWAP suka kaiwa hari musulmi ne tunda sun fi kai hare-hare a Arewa inda galibi musulmi.

“Don haka, musulmi ne wadanda rikicin ya fi shafa a Najeriya. Babu wani alkallami da zai canja hakar koda daga ina ya fito,” in ji shi.

Ya cigaba da cewa ana ganin kamar an fi kashe kirista ne domin irin yadda suke birne gawarsu, “kiristoci a Najeriya suna nuna gawarwarki har suna jinkirta jana’iza da kwanaki ko watanni amma musulmi na birne nasu nan take ne ba tare da zuzuta abin ba. Dabara ce ta kyamara.”

Shugaban na MURIC ya ce karya ne ikirarin da suke yi cewa gwamnatin Najeriya bata kare hakkin mutane su yi addinin da suke so.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here