An Musanta Rahoton Gidan Rediyo,Kan karbar kudin Fansa da Jami’an Tsaro keyi.

 

Shugaban kasuwar siyar da shanu ta kwanar Dangora dake Kano, Sulaiman Yunusa Gwarmai ya bayyana cewar wani rahoto da wani gidan rediyo a jihar ta Kano.

ya kawo dake zayyana cewar wasu Jami’an ‘Yan sanda na tsare fulani masu siyar da shanu,su karbi kudi masu tsoka a wajen su,wani shudaddan al’amari ne.

Yayin zantawa da Jaridar Arewa Agenda,lokacin da take gudanar bincike,Gwarmai ya bayyana cewar rahoton da wancan gidan rediyon ya kawo kan wancan lamari,kwata kwata sha’anin bashi da ruwa da Kasuwar Dangora,hasalima wancan lamarin a Kasuwar Kwanar Dawaki abun ya faru,dake kusa da cikin gari.

Ya bayyana cewar hakika Kasuwar ta Kwanar Dangora a baya ta fuskanci wasu kalubalulluka makamantan wadannan inda wasu jami’ai masu kaki ke masu barazana da kutse cikin lamuran kasuwancin su,har ta kai ga sun fara zurfafa tunanin rufe Kasuwar dugurungum domin kuwa a cewar su turar ta kai bango.

amma bisa tsoma hannun hukumar ‘Yan sandan Jihar Kano,bisa jagorancin kwamishina CP Habu Sani da shugaban sashen SARS na wancan,tuni wannan muguwar ta’ada ta kau,a yayin da suke cigaba da harkokin su na kasuwancin cikin lumana da kwanciyar hankali.

” Kamar yadda kuke gani ana ta hada hada dakai kawo a wannan kasuwa a dai dai wannan lokaci,da ace kwanakin baya kuka zo, mutane kadan zaku gani anan,lokacin da rashin tsaro da kalubale suka fara yimana dabaibayi mun kai koke zuwa ga Mai Gari,inda ya isar zuwa ga hakimi,aka isar zuwa ga DPO.

DPO ya garzaya da maganar zuwa ga OC na SARS, OC na SARS hakika ya dau matakan da suka dace,duk wasu jami’an hukomomi da suka karbi kudin mutane,yasa an dawo musu dashi,kuma ya umarci jami’an ‘Yan sanda.

cewar duk ranar da wannan kasuwa take ci suzo domin inganta tsaro yadda ya kamata,kun gansu da idanuwan ku a hanyar shigowa wannan kasuwa,hakika muna gudanar da kasuwancin mu yanzu cikin kwanciyar hankali da walwala.” Gwarmai ya bayyana.

Ya jaddada rashin jin dadinsa matuka kan yadda wani,wanda yace basu ma sanshi ba ya danganta kansa da kasuwar su ya fito gidan rediyo yana mai wannan ikirari.

” Kwatsam muka ji wani rahoto a shirin Inda Ranka wani yana mai danganta faruwar wani lamari ga wannan kasuwa,hakika irin wannan lamarin ya faru da wasu daga cikin ‘yan kasuwar mu.

sau kusan hudu ko biyar can wani lokaci kafin daukar mataki daga hukuma,amma wannan kam ba anan ya faru ba,acan Kwanar Dawaki ne.

Ina amfani da wannan dama in mika godiya ta musamman ga hukumar jami’an ‘Yansanda ta jihar Kano bisa kokarin su da jajircewar su kan shawo mana matsaloli masu yawa,bamu da wani korafi garesu sai sam barka.

Gwarmai ya jaddada.

A cewar sa,mai magana da yawun hukumar ‘Yansanda ta Jihar Kano,DSP Abdullahi Haruna Kiyawa,ya bayyana cewar ana samun wasu bata gari da suke sajewa a matsayin ‘yansanda suna aikata barna irin wadannan.

” Bada jimawa ba mun kama wasu biyu,daya daga cikin su yayi sojan gona a matsayin dansanda yaje yana neman cire wani bata garin dan’uwansa da aka kama da wasu bindigogi.

Maganar gaskiya tun lokacin da akai wancan rahoton, hakika ya sanyaya kuma ya karya gwiwar manyan jami’an mu kwarai da gaske.” Kakakin ‘Yansanda ya bayyana.

Kakakin na ‘Yansanda ya bayyana cewar wanda yai rahoton bai tabo bangaren hukumar ‘Yansanda ko kuma masu siyar da shanun ba kafin sakin wancan rahoto.

Jaridar Arewa Agenda ta binciko cewar sati biyu da suka wuce wata sananniyar gidan rediyo a wani sanannen shiri daga wani sanannen dan jarida sun saki rahoto dake nuni da cewar wasu jami’an hukumar SARS(Wanda yanzu an rushe su) suna tahowa daga jihar Abuja suna kama Fulani masu siyar da shanu su tsare su,ba bisa ka’ida ba su kuma karbi kudade masu yawa daga garesu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here