Elon Musk Zai Bayar da Kyautar Dala Miliyan ɗaya Don a Zaɓi Trump

 

Mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya Elon Musk ya ce zai riƙa bayar da kyautar dala miliyan ɗaya a duk rana daga yanzu har zuwa ranar zaɓe – 5 ga watan Nuwamba, ga mai zaɓe ɗaya, a muhimman jihohin da za su tabbatar da wanda zai ci zaɓen Amurka.

Za a zaɓi wanda ya yi nasarar cin kuɗin ne daga waɗanda suka sanya hannu na goyon baya ga wata takarda kan kundin tsarin mulkin Amurka, wadda Elon Musk ke jagoranta mai laƙabin AmericaPAC, wadda ke goyon bayan Donlad Trump na jam’iyyar Republican, a fafutukarsa ta sake komawa kujerar mulkin ƙasar.

A ranar Asabar da daddare ne aka bai wa mutum na farko da ya ci kuɗin a Pennsylvania, sannan a ranar Lahadi ma aka bai wa wani.

Gwamnan jihar Pennsylvania Josh Shapiro, ɗan Democrat wanda ke goyon bayan mataimakiyar shugaban ƙasa, kuma ƴar takarar jam’iyyar ta Democrat, Kamala Harris, ya kira tsarin na Mr Musk abin damuwa sosai.

A tattaunawarsa da kafar yaɗa labarai ta NBC Shapiro ya ce kamata ya yi jami’an tsaro su duba wannan lamari ya bayar da kuɗin ga masu zaɓe.

Gasar ta tsaya ne ga masu zaɓe a jihohin Pennsylvania, da Georgia, da Nevada, da Arizona, da Michigan, da Wisconsin da kuma North Carolina, waɗanda dukkaninsu jihohi ne da za su raba gardama a zaɓen shugaban Amurkar.

Ƙwararre a kan dokokin zaɓe, kuma malami a jami’ar California, Los Angeles (UCLA), Rick Hasen, ya rubuta a shafinsa na intanet cewa yana ganin abin da Mr Musk ke yi haramun ne ƙarara.

Dokokin tarayya na Amurka sun ayyana cewa duk wanda ya biya kuɗi ko ya yi tayin bayar da kuɗi domin wani ya yi rijista ya yi zaɓe ko kuma don mutum ya yi zaɓe, mutumin na fuskantar haɗarin hukuncin tarar dala dubu 10 ko hukuncin ɗaurin shekara biyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here