Ramadan: Shugaba Buhari ya yi Kira ga Musulmai su Ciyar da Talakawa Abinci
Bayan sanarwar ganin watar azumin Ramadana mai alfarma, Shugaba Buhari ya taya Musulman Najeriya murna.
A sakon maraba da Ramadanansa, Shugaban kasan ya yi kira ga Musulmai su ciyar da talakawa abinci.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad ya sanar da ganin wata da kuma kaddamar watar azumi
Abuja – Shugaba Muhammadu Buhari ya taya al’ummar Musulman Najeriya murnan ganin watar Ramadana bayan sanarwan Mai Alfarma Sarkin Musulmi.
Read Also:
A sakon taya murnarsa, shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da wannan dama wajen ciyar talakawa da marasa galihu.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma’a, 1 ga watan Afrilu, 2022.
Buhari yace lokacin azumi wani dama ne dake nunawa masu hannu da shuni irin yunwan da talaka ke fama da shi kulli yaumin.
Buhari ya shawarci Musulmai su daina asarar abinci da almubazzaranci yayinda wasu ke fama da yunwa da kunci.
Ya yi kira ga Musulmai su rika tunawa da makwabtansu, talakawa da marasa karfi.