Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci ya Yabawa Gwamnatin Kaduna Kan Rusa Gidan Otel
Gwamnan jihar Kaduna ta sha yabo da suka kan ruba gidan da aka shirya casu.
Yayinda wasu ke cewa bai kamata ya rusa ba tukun, wasu sunce yayi daidai.
An damke mammalakin gidan Otel din da wadanda suka shirya taron.
Majalisar koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ta jinjinawa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i bisa rusa otel din da aka shirya banbadewa zindir makon da ya gabata.
Majalisar ta ce ire-iren wadannan laifukan ke gadarwa al’ummar Najeriya fushin Allah.
Hakazalika ta yabawa gwamnatin jihar bisa damke wadanda suka shirya bikin.
Read Also:
A jawabin da shugaban majalisar na jihar Kaduna, AbdurRahman Hassan, ya saki, ya ce ire-iren wadannan taron shaidancin ke haifar zuba da jini da ake yi ta hanyar garkuwa da mutane, fashi da makami.
“Ko shakka babu, ire-iren wadannan abubuwa ya gadar mana fushin Allah (SWT) da muke fuskanta yanzu,” wani sashen jawabin yace.
“Lalacewar tarbiyyanmu ke haifar da zub da jinin da akeyi ta hanyar garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran laifuka.”
“Yayinda muke yabawa gwamnatin jihar Kaduna kan wannan abun alkhairin da tayi, muna kira da gwamnatin ta zuba ido kan sauran wuraren da ake ire-iren wadannan abubuwa a jihar, irinsu Ajagunle, dake Maiduguri Road, karamar hukumar Kaduna ta Arewa, inda akwai gidajen tsiraici.”