Mutane 10 Sun Rasa Rayukansu Sakomakon Harin Boko Haram a Jahar Borno
An tabbatar da mutuwar mutane 10 sakamakon harin da Boko Haram ta kai Damasak.
Mustapha Bako Kolo, shugaban karamar hukumar Mobbar a jahar Borno ne ya bayyana hakan.
Baya ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ya ce akwai wasu mutane kuma da suka jikkata An tabbatar da rasuwar fararen hula 10 a harin da yan Boko Haram suka kai a daren ranar Talata a garin Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar na jahar Borno.
Shugaban karamar hukumar Mobbar, Mustapha Bako Kolo ne ya bayyana hakan kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Read Also:
Wasu da ke zaune a sansanin yan gudun hijira da ba a tabbatar da adadinsu ba suma sun jikkata sakamakon harin a cewar Kolo.
Duk da cewa dakarun sojojin saman Nigeria da sojojin sama sun dakile harin, wasu mutane fararen hula da dama sun jikkata.
A cewar majiyoyi, yan ta’addan sun afka garin a motocci suka nufi inda sansanin sojoji ya ke a Damasak a yayin da mutane suka rika tserewa.
Harin na daren jiya a Damasak shine na biyu a cikin mako guda.
Yan ta’addan sun wallafa bidiyon harin da suka kai a karshen mako a Damasak inda suke kona gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya da wuraren ajiye abinci.
Kawo yanzu da aka wallafa wannan rahoton, rundunar sojojin Nigeria bata yi tsokaci game da batun ba.