Mutane 2 Sun Rasa Rayukan su Sakamakon Fashewar Iskar Gas a Dakin Karatun Obasanjo Dake Ogun
Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar iskar gas a dakin karatun shugaban kasa Obasanjo da ke Ogun.
Rahotanni sun bayyana cewa makinai ne ke kokarin saka iskar gas a na’urar sanyaya daki, AC, kwatsam dai abin ya fashe.
Tuni dai jami’an hukumar kashe gobara na jihar sun isa wurin da abin ya faru domin bada gudunmawarsu wurin kashe wuta.
Read Also:
A kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jahar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.
Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.
Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jahar Ogun Gbenga Daniel ne.
Fashewar gas din a OOPL ya faru ne misalin karfe 11 na safe a wurin taro na Marque Event Centre da ke harabar dakin karatun na shugaban kasa.
Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa makanikai suna zuba gas ne cikin na’urar sanyaya daki wato AC a lokacin da ya fashe.
“An tabbatar da rasuwar mutane biyu,” ma’aikacin a OOPL ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng.