Yadda Kimanin Mutane 50 Suka Rasa Rayukansu a Jahar Legas

 

Kimanin mutane 50 ne aka ruwaito sun rasu bayan hallartar casun birthday a jahar Legas.

Wani dan damfara ta intanet wato Yahoo Boy ne ya hada casun a Legas a cewar rahotanni.

A cewar wani @pelumiawotedu a Twitter, lamarin ya faru ne a Unguwar Alagboke Akute a Legas Wani matashi a dandalin sada zumunta ya yi alhinin rashin abokansa bayan mutane 50 sun mutu a wani yanayi mai daure kai bayan hallartar casun da wani da ake zargin ‘Yahoo boy’ ne ya hada.

Lamarin mai ban tsoro ya faru ne a Alagbole Akute, jahar Legas a cewar wani mai amfani da Twitter @pelumiawotedu.

Wani matashi mai damfara ta intanet ‘yahoo boy’ a cewar majiyoyi a dandalin sada zumunta, ya shirya gagarumin casu domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa Lahadi biyu da suka gabata inda abokansa 50 suka hallarci taron.

Sai dai dukkansu 50 sun mutu cikin wani yanayi mai daure kai bayan hallartar casun da aka kashe dare ana yi. Wani mai amfani da Twitter @ysquare_r shima ya yi ikirarin makwabcinsa ta rasa abokinta, danta da wani yaro sakamakon hallartar casun.

Ya kara da cewa wani mutum a layinsu da abokansa hudu da suka hallarci casun suma duk sun mutu.

A cewar @ysquare, a lokacin da ya wallafa rubutun, mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya kuma akwai yiwuwar wasu sun mutu bayan su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here