Mutane na Cikin Halin Talauci a Najeriya – Ministan Noma
Karamin Ministan noma ya bayyana halin da Najeriya ke ciki game da abinci.
Shi kuwa Ministan Noma, Nanono, yace akwai bakar talauci a Najeriya.
An gudanar da taron ciyar da Najeriya a Abuja ranar Litinin.
Abuja – Karamin ministan noma da raya karkara, Mustapha Shehuri, ya bayyana cewa Najeriya ka iya fadawa halin karancin abinci saboda babu tsari mai karfi na tsaron abinci.
Shehuri ya bayyana hakan ranar Litinin a ‘Taron Ciyar Da Najeriya’ da akayi a birnin tarayya Abuja. rahoton TheCable.
Shehuri, wanda ya samu wakilcin Dirakta a ma’aikatar noma, Karima Babangida, ya bayyana cewa wannan taro zai taimakawa ma’aikatar wajen sake duba raunin tsarin abinci a Najeriya don karfafashi.
Read Also:
Yace ma’aikatar shirye take da samar da sabon tsarin tsaron abinci da zai tabbatar cewa dukkan yan Najeriya zasu samu abinci kuma mai inganci.
Yace:
“Wannan shine dalilin da yasa ake shirye-shirye daban-daban na tsaron abinci a ma’aikatar a sassan Najeriya.”
Yace idan ana son a samu tsari mai inganci, wajibi ne Najeriya ta shawo kan matsalar yunwa, samar da ingantattun abinci da kuma daina asarar abinci.
Mutane na cikin halin talauci a Najeriya
Duk a taron, Ministan Noma, Muhammad Sani Nanono, ya ce ko Najeriya ta samar da isasshen kayan abinci, wajibi ne wasu su kwana cikin yunwa saboda basu da kudin sayen abinci.
Nanono yace wannan matsalar rashin aikin yi ne kuma babban kalubale ga kasar nan.
Yace:
“Idan bamu mayar da hankali kan wannan babbar matsalar rashin aikin yi cikin matasa da kuma sama musu aikin yi ba, babu abinda mukeyi.”