Mutane(8,730) Sun Samu Gyaran Ido da Magani da Gilashi Kyauta a Kwanaki (4)
A yau ne aka kammala gudanar da aikin gyaran ido da bada magani da gilashi kyauta wanda ƙungiyar matasa musulmai ta Duniya, “World Assembly Of Muslim Youth”, (WAMY), da haɗin gwiwar gidauniyar Malam Inuwa, da haɗin kan gwamnatin Jihar Jigawa su ka gudanar ga al’ummar Jihar Jigawa a Asibitin garin Haɗejia.
Jimillar mutane dubu takwas da ɗari bakwai da talatin, 8730, ne su ka samu nasarar cin gajiyar wannan tsari wanda aka shafe tsawon kwanaki huɗu ana gudanarwa, 21-24 Nuwamba, 2021).
1. Jimillar Gilashin Ido da aka raba kyauta a cikin waɗannan kwanaki (4) su ne guda (500):-
A rana ta farko:- An ba wa mutane 229 Gilashi.
A rana ta biyu:- An ba wa mutane 148 Gilashi.
A rana ta uku:- An ba wa mutane 123 Gilashi.
A rana ta huɗu:- Babu gilashi ya riga ya ƙare.
2. Jimillar mutanen da aka rabawa magani kyauta a kwanaki huɗu, su ne mutum dubu bakwai da ɗari biyar da casa’in da uku: (7,593):-
Rana ta farko:- An ba wa mutane (450).
Rana ta biyu: An ba wa mutane (2,258).
Rana ta uku:- An ba wa mutane (4,885).
Rana ta huɗu: Ba a raba ba, saboda ya ƙare.
3. Jimillar adadin mutanen da su ka amfana da samun aikin tiyatar ido kyauta a waɗannan jimillar kwanaki huɗu, su ne mutum (637):-
Rana ta farko: An yi wa mutane (50).
Rana ta biyu: An yi wa mutane (187).
Rana ta uku: An yi wa mutane (350).
Rana ta huɗu: An yi wa mutane (50).
Gabaɗaya jimillar mutanen da su ka amfana da wannan shiri na gyaran ido da bada magani da gilashi kyauta a Jihar Jigawa, su ne: (8,730).
Jim kaɗan da kammala shirin a wannan rana, sai kuma aka gudanar da ɗan ƙwarya-ƙwaryan taron yi wa juna barka da karrama jami’an lafiyar da su ka taka rawa cikin aikin ta hanyar raba musu Littafi mai tsarki, (Alqur’ani).
Read Also:
A jawabin da ya gabatar a ya yin rufewa da karramawar, shugaban ƙungiyar ta (WAMY) a Najeriya, Dakta Isham Muhammad, ya bayyana matuƙar farin cikinsa da samun sa’ar farawa da kammala shirin cikin nasara, inda daga bisani ya bayyana godiya ga gwamnatin Jihar Jigawa da gidauniyar Malam Inuwa haɗi da hukumar gudanarwa ta asibitin Haɗejia, da fadar Sarki, inda daga ƙarshe ya bayyana farin ciki da irin tarya da karamcin da ya samu a wannan Jiha.
Shi ma a nasa jawabin, Dakta Bihlali Abdallah, likitan da ya zo daga birnin Riyad na ƙasar Saudiyya, ya kuma gudanar da aikin tiyatar ido a cikin wannan shiri, ya bayyana cewa wannan shi ne zuwansa na biyu Nageriya, inda ya bayyana ƙasar a matsayin ƙasar da al’ummarta su ka san darajar baƙi wanda hakan na daga cikin dalilan da su ka ƙara masa ƙarfin gwiwar dawowa ƙasar a wannan karo na biyu bayan da ya taɓa zuwa Jihar Katsina a wasu lokuta da su ka shuɗe ya gudanar da irin wannan aikin agaji.
Haka zalika, Dakta Bihlali, ya ƙara da cewa abu na biyu da ya ƙara masa ƙaimi wajen sake zuwa Nageriya shi ne yadda ya ga al’umma su na matuƙar buƙatar aikin ido duba da yadda ya ga manyan mutane maza da mata su na turereniyar zuwa neman samun wannan aiki kyauta, inda ya kuma ƙara da cewar a kowane lokaci a shirye ya ke domin ya sake dawowa ya cigaba da wannan aikin jinƙai ga ƴan Nageriya.
Da ya ke gabatar da nasa tsokacin, Dakta Usman Muhammad, na sashen lafiyar ido a babbar Asibitin Haɗejia, ya bayyana godiya, jinjina da yabo ga duka ɓangarorin da su ka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen gudanar da wannan aiki na agaji da taimako da jinƙai ga al’umma.
Shi ma a cikin nasa jawabin, Dakta Usaini Muhammad Baban, shugaban gidauniyar Malam Inuwa, wacce mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya assasa ya ke kuma jiɓintar lamarinta, ya bayyana farin ciki da godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki cikin wannan aikin alkhairi tare da fatan Allah Ya sakawa kowa da alkhairi.
Ɗumbin jama’a da su ka amfana da wannan aikin alkhairi da sauran al’umma duka, sun yi matuƙar godiya da farin ciki marar misaltuwa tare da fatan Allah Ya ba da ladan wannan aiki.
Laraba, 24 ga watan Nuwamba, 2021.