Abinda Zamu yi da ‘Yan Mata 22 da Muka Sace a Jahar Neja – Mahara

Wasu yan ta’adda da ake tsammanin mayakan Boko Haram ne sun sace yan mata 22 a wani kauyen jahar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shaida wa mutanen kauyen cewa ba zasu cutar da su ba, aurensu za su yi.

Tun a bayan dai kuma a lokuta da dama, Gwamnan Neja ya yi korafin cewa mayakan Boko Haram sun fara kafa sansani a jahar.

Niger – Wasu yan ta’adda da ake zaton mayakan Boko Haram ne, sun kai hari kauyen Kurebe dake karamar hukumar Shiroro a jahar Neja.

Tribune Online ta rahoto cewa maharan sun yi awon gaba da yan mata 22 yayin famakin, wanda ya auku ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa yan matan da maharan suka sace suna tsakanin shekara 15 da 17 kuma sun shaida wa mutanen ƙauyen auren su zasu yi.

Ya mutane suka ji da lamarin?

Ɗaya daga cikin shugabannin ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace yan ta’addan sun umarci a cire matan daga makaranta saboda zasu aure su.

Ya kara da cewa sun yi mamaki da maharan suka zo ranar Alhamis suka ɗauki yan matan, ba tare da jami’an tsaro sun kawo ɗauki ba.

Kazalika ya bayyana cewa shugaban tawagar yan ta’addan, Malam Sadiku, shine yake jagorancin kai hari yankin, kuma yana wa’azi kan tsattsauran ra’ayin musulunci.

Yace:

“Suna cin karen su babu babbaka a yankin, amma da zaran sun ga wata bakuwar fuska, to ko dai su sace shi ko kuma su kore shi daga yankin. Mun kai kukan mu ga hukumomi lokuta da dama.”

Dagaske mayakan Boko Haram ne?

A kwanakin baya, gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yi korafin cewa wasu tawagar yan ta’adda dake da alaka da Boko Haram sun fara kafa tutarsu a Kaure, wanda ke kusa da Kurebe.

Kazalika shugaban karamar hukumar Shiroro, Kwamaret Suleiman Dauda Chukuba, ya yi korafi kan ayyukan wannan tawaga, kuma ya nemi a ɗauki mataki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here