Mutane 2,107 Sun Samu Gyaran Ido da Magani da Gilashi Kyauta a Kwanaki 6
A yau ne alhamis aka kammala gudanar da aikin gyaran ido da bada magani da gilashi kyauta wanda Gidauniyar kasar Qatar da haɗin gwiwar gidauniyar Malam Inuwa, su ka gudanar ga al’ummar Jihar Jigawa a Asibitin garin Gumel.
Jimillar mutane dubu biyu da dari da guda bakwai, 2107 ne su ka samu nasarar cin gajiyar wannan tsari wanda aka shafe tsawon kwanaki shidda ana gudanarwa, 11-16 June, 2022).
1. Jimillar Gilashin Ido da aka raba kyauta a cikin waɗannan kwanaki (6) su ne guda (594):-
A rana ta farko:- An ba wa mutane 200 Gilashi.
A rana ta biyu:- An ba wa mutane 286 Gilashi.
A rana ta uku:- An ba wa mutane 104 Gilashi.
A rana ta huɗu:- An bawa mutane 04 Gilashi.
A rana ta biyar:-Babu gilashi ya riga ya ƙare.
A rana ta shidda:-Babu gilashi ya riga ya kare.
2. Jimillar mutanen da aka rabawa magani kyauta a kwanaki shidda, su ne mutum dubu daya da ashirin da biyar : (1025):-
Read Also:
Rana ta farko:- An ba wa mutane (286).
Rana ta biyu: An ba wa mutane (291).
Rana ta uku:- An ba wa mutane (356).
Rana ta huɗu: An ba wa mutane(92)
Rana ta biyar:-Ba a raba ba, saboda ya ƙare.
Rana ta shidda:- Ba a raba ba, saboda ya kare.
3. Jimillar adadin mutanen da su ka amfana da samun aikin tiyatar ido kyauta a waɗannan jimillar kwanaki shidda, su ne mutum (468):-
Rana ta farko: Ba ayi tiyata ba saboda ana shirye shiryen kayan aiki:-(00)
Rana ta biyu: An yi wa mutane (38).
Rana ta uku: An yi wa mutane (180).
Rana ta huɗu: An yi wa mutane (100).
Rana ta biyar: An yi wa mutane (150).
Rana ta shidda: ba’ayiba domin shirin tafiya(00).
Gabaɗaya jimillar mutanen da su ka amfana da wannan shiri na gyaran ido da bada magani da gilashi kyauta a Jihar Jigawa, su ne: (2,107).
Bayan kammala dukkanin shirye shirye na tafiya gida wadannan Gidauniya guda biyu ta Qatar charity foundation da ta Malam Inuwa foundation ta kai ziyara ga mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmad Muhammad Sani(CON), inda Mai martaba sarki ya nuna farin ciki da murnarsa ga wadannan Gidauniya ,ya kuma yi addu’ar fatan alkairi da samun ire irensu masu yawa a nan gaba don kara taimakawa al’umma.
Muna rokon Allah ya bawa dukkanin marassa lafiyar mu lafiya , Allah kuma ya hadamu a cikin ladan wannan babban aiki na alkairi????
~ Buhari Ya’u Gumel
16/6/2022.