Gwamna Masari ya yi Kira ga Mutane Kan su Mallaki Bindiga Don Kare Kansu Daga ‘Yan Ta’adda

 

Gwamna Masari na jahar Katsina ya shaida wa jama’arsa cewa, kowa ya mallaki bindiga don yakar barayi.

Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi wajen jajantawa iyalan wasu mutane 10 da suka mutu sanadiyyar jami’an kwastam.

Gwamnan ya ce, tunda ‘yan bindiga na iya sayen bindiga su aikata ta’addanci, to ‘yan kasa ma za su iya saye don kare kai.

Gwamna Aminu Bello Masari na jahar Katsina ya yi kira ga mutanen da ke zaune a yankunan da ke da yawan ‘yan bindiga da su mallaki makamai su kare kansu daga ta’addanci.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na yada labarai ga gwamnan, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar, wanda Daily Trust ta samu.

Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su mika wuya ga ‘yan bindiga ba tare da wani yunkuri na kare kansu ba, lura da cewa tsaro aikin kowa ne.
Channels Tv ta ruwaito gwamnan na cewa:

“Dole ne dukkan mu mu tashi tsaye don tunkarar kalubalen rashin tsaro, kada mu zauna mu kalli wasu mutane suna sayen bindigogi suna kai hari a gidajen mu, mu ma ya kamata mu sayi bindigogin mu kare kan mu.”

Meye gwamnati ke yi game da mutuwar mutane 10 sanadiyyar jami’an kwastam?

Legit Hausa ta gano Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a garin Jibia ranar Talata 17 ga watan Agusta, lokacin da ya kai ziyarar jajantawa kan rasuwar mutane 10 da wasu jami’in hukumar kwastam ta Najeriya suka yi sanadiyya a ranar Litinin yayin tuki a kan aiki.

Da yake magana game da mutuwar mutanen 10, Gwamna Masari ya tabbatar wa mutane cewa gwamnati tana bin dukkan matakan da suka dace na shari’a don neman hakkin iyalan mamatan, da kuma wadanda suka sami raunuka daban-daban.

Ya kara da cewa tuni aka tuntubi masana harkar shari’a don ba da shawara kan hanyar da za a bi don tabbatar da gaggauta warware matsalar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here