Bayan Kwace Mulki a Afghanistan: Sojojin Amurka Sun Gana da Shugabannin Taliban

 

A can kasar Afghanistan, sojojin Amurka sun gana da shugabannin Taliban don fayyac wani batu.

Batu ne kan yadda kasar Amurka za ta tattara dakarunta da kuma Amurkawan da ke cikin kasar.

Har yanzu dai Taliban na ci gaba da cewa, ita ba abinda ke gaban ta illa wanzar da zaman lafiya a kasar.

Afghanistan – Amurka ta bayyana cewa dakarunta sun gana da shugabannin Taliban da suka kwace mulki a kasar Afghanistan, in ji Aminiya.

Kakakin Sakataren Tsaron Amurka, John Kirby, ya ce kwamandojin kasar da ke filin jirgin sama na Kabul, babban birnin Afghanistan na ganawa da Taliban “a matakin Afghanistan, muna kuma tattaunawa da su kan kwaso Amurkawa”.

The Columbian ta ruwaito cewa, Kirby shaida wa ’yan jarida a Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) cewa:

“Nan gaba ne za a san me zai faru, amma tabbas kwamandojinmu suna magana da shugabannin Taliban domin kammala aikin da suka je yi a can.”

Hakazalika, Janar Frank McKenzie, shugaban rundunar Amurka, ya gargadi jami’an Taliban cewa sojojin Amurka za su mayar da martani da karfi don kare filin jirgin sama idan hakan ya kama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here