Ambaliyar Ruwa: Mutane 3 Sun Mutu a Babban Birnin Tarayya Abuja

 

Ambaliyar ruwa ta yi barna a rukunin gidajen Trademore a Luge babban birnin tarayya Abuja.

Mazauna unguwar sun ce ambaliyar ruwar ya fara ne a ranar Litinin bayan ruwan sama mai karfi da aka yi.

Kawo yanzu an gano gawarwakin mutane uku sannan ruwan ta lalata motocci da kayayyakin al’umma da dama.

FCT, Abuja – A kalla gawarwakin mutane uku ne aka gano a safiyar ranar Litinin a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, Premium Times ta rawaito.

Rahoton na Premimum Times ya ce mazauna unguwar sun ce ambaliyar ruwan ya fara ne a safiyar ranar Litinin bayan ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya.

Ambaliyar ruwar ya yi sanadin bacin motocci da wasu kayayyakin mutane da dama a unguwar.

Jami’an hukumar kwana-kwana na birnin tarayya Abuja sun isa wurin a safiyar ranar Litinin domin kai wa mutane dauki.

A kan samu irin wannan ambaliyar ruwar a unguwar a duk damina na kowanne shekara.

Ku saurari karin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here