Mutane 7 Sun Mutu Bayan Sun Ci Tsire a Jahar Abia
Wasu iyalai sun bakunci lahira bayan da suka ci suya da mai gidan ya sayo a kasuwa.
Rahoto daga jahar Abia ya bayyana cewa, akalla mutane bakwai ne suka mutu bayan cin naman.
Biyu daga cikin iyalan sun tsira, kuma suna karbar kulawar asibiti a Asibitin Tarayya na Umuahia.
Abia – Wasu iyalai mutum bakwai sun mutu bayan sun ci suyan kasuwa da ruwan jus a wani yankin Umuahia, babban birnin jahar Abia, Daily Trust ta rawaito.
Lamarin ya faru ne a Umueze Umuakanu da ke karamar hukumar Umuahia ta Arewa a jahar.
Read Also:
Rahotanni sun ce, dukkan iyalan, ciki har da iyalan da suka zo hutu sun ci suyan wanda mai gidan, Mista Jessey, ya saya ya kawo gida.
An ce sun fara amai bayan sun ci naman da ake zargin yana dauke da guba.
Yanzu haka mutum biyu da suka tsira a cikin iyalan suna karbar magani a Asibitin Tarayya dake Umuahia, yayin da aka ajiye mamatan a dakin ajiye gawa na asibitin.
A halin da ake ciki, gwamnatin jahar Abia ta ce ta samu rahoto kan abin bakin cikin da ya faru.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai, Cif John Okiyi Kalu ya fitar, ya ce Gwamna Okezie Ikpeazu ya umarci hukumomin asibitin da su kula da mutanen da suka tsira wajen jinya da kuma fitar da matattun don tabbatar da cikakken bincike.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga ‘yan kasa da mazauna yankin da su ci gaba da taka tsantsan wajen sayen abinci tare da ci gaba da bin doka.