Mutane 30 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Tankar Mai a Neja

 

Neja – Sama da mutane 30 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon fashewar tankar mai a karamar hukumar Agaie ta jihar Neja.

An bayyana cewa tankar man ta yi karo ne da wata motar tirela dauke da matafiya da shanu daga karamar hukumar Wudil ta jihar Kano.

Tanka ta fashe, mutane sun mutu

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) Abdullahi Baba-Arab ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wata sanarwa, inji rahoton The Punch.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 12:30 na rana a kan titin Lapai-Agaie mai nisan kilomita 2 daga yankin Dendo a karamar hukumar Agaie.

A cewar Baba-Arab, sama da shanu 50 ne suka babbake da ransu yayin da wasu motoci guda biyu; babbar motar daukar karafuna da wata motar daukar kaya suka kone a cikin gobarar.

NSEMA ta yi bayanin iftila’in

Sanarwar ta NSEMA ta ce:

“NSEMA ta samu rahoton fashewar wata tankar mai a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024 da misalin karfe 12:30 na rana a kan titint Lapai-Agaie, kilomita 2 daga Dendo a Agaie.

“Lamarin ya faru ne a lokacin da wata tankar fetur ta yi karo da wata motar tirela da ke dauke da matafiya da shanu daga Wudil a jihar Kano da ke kan hanyar zuwa Legas.

“Sama da mutane 30 ne aka tabbatar sun mutu, tare da babbakewar shanu sama da 50 da ransu. Har yanzu tawagar NSEMA tare da haɗin gwiwar LGEMCs suna wurin da abin ya faru.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here