Mutane 3 Sun Mutu a ƙasar Masar Sanadiyyar Harbin Kunama

 

Rahotanni daga Masar na cewa kunamu sun kashe mutum uku a kudancin birnin Aswan bayan ruwan sama mai ƙarfi ya jawo su kan tituna da cikin gidajen mutane.

Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta tabbatar da cewa aƙalla mutum 450 ne kunama ta harba.

Ruwan da aka yi a kusa da Kogin Nilu a ranar Juma’a na da ƙarfi ƙwarai kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Dama ruwan sama mai ƙarfi ya saba sharo kunamu kan tituna, a wani lokacin ma har da macizai.

Tuni gwamnatin ƙasar ta aika da magungunan kashe dafin kunama da macizai zuwa asibitoci da ke ƙauyukan da ke gefen tsaunuka da sahara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here